Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-12 16:10:03    
Ya kamata gwamnatin kasar Sin ta kara daukar matakai domin fuskantar matsalolin aikin kawo albarka cikin kwanciyar hankali

cri
Wakilan jama'a da ke halartar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ake yi yanzu a birnin Beijing sun bayyana cewa, ya kamata gwamnatin kasar Sin ta kara daukar matakai domin fuskantar matsanancin halin da ake ciki yanzu wajen aikin kawo albarka cikin kwanciyar hankali.

Har ila yau halin da ake ciki a kasar Sin wajen aikin kawo albarka cikin kwanciyar hankali yana da tsanani. Yawan mutanen da suka mutu a shekarar da ta wuce sabo da hadarurrukan aikin kawo albarka ya kai kusan dubu 130 a kasar Sin. Wakilan majalisar sun bayyana cewa, ya kamata gwamnatin kasar ta kara daukar matakai don sa kaimi ga mahakan kwal da sauran masana'antun da abin ya shafa da su kara ware kudi da yawa domin aikin kawo albarka cikin kwanciyar hanakali, ta yadda za a tabbatar da kwanciyar hankali wajen aikin. Sa'an nan kuma, ya kamata sassan da abin ya shafa su kara mai da hankali don yin horo da ba da ilmi ga mutane masu sana'o'in hadarurruka, ta yadda za a rage yawan hadarurrukan da za su yiwu su faru. (Umaru)