|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2006-03-11 21:15:04
|
Hukumomin binciken shari'a na kasar Sin sun kara karfin yaki da cin hanci da rashawa
cri
Jia Chunwang, shugaban hukumar koli ta binciken shari'a ta kasar Sin ya fayyace a ran 11 ga wata a nan birnin Beijing cewa, a bara, gaba daya ne hukumomin binciken shari'a na kasar Sin suka bin bahasin ma'aikatan hukumomi sama da dubu 4 wadanda ke da laifuffukan cin hanci da rashawa da kuma yin sakaici da aiki da karya hakkin saura, sabo da haka, aka ingiza aikin yaki da cin hanci da rashawa a nan kasar Sin sosai da sosai.
A ran nan, taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya saurari rahoton da Mr.Jia Chunwang ya yi dangane da aikin hukumar koli ta binciken shari'a ta kasar Sin.(Lubabatu Lei)
|
|
|