Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-11 20:54:02    
Hukumar yin tuhuma da yanke hukunci ta kasar Sin za ta kara karfin shari'a na kiyaye ikon mallakar ilmi

cri
A ran 11 ga wannan wata a nan birnin Beijing, shugaban babbar kotun jama'ar kasar Sin Xiao Yang ya bayyana cewa, kotunan kasar Sin na matakai daban daban za su ci gaba da kara karfin shari'a na kiyaye ikon mallakar ilmi.

A wannan rana, lokacin da Xiao Yang ya bayar da rahoto kan aikin babbar kotun jama'ar kasar Sin ga taron shekara shekara na Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya bayyana cewa, a shekarar da ta shige, babbar kotu ta kara karfinta na yin tuhuma da yanke hukunci kan laifufuka na keta ikon samun takardar iznin mallaka da shahararrun almomin kamfannoni da internet da ikon wallafa wake-wake da shirye-shiryen TV da dai saruansu.

A shekarar da muke ciki, kotunan kasar Sin na matakai daban daban za su kara karfin yin tuhuma da yanke hukunci kan laifufukan keta ikon mallakar ilmi da kuma yanke laifufukan keta ikon mallakar ilmi bisa shari'a da gaske da kuma yanke hukunci kan aikace-aikacen yin kayayyakin jabu da sata fasahar kera kayayyaki da dai sauransu da kuma daukaka karar da aka yi kan rikicin rajistar sunaye a internet da ikon rike da almomin kamfannoni da dai sauransu, sa'anan kuma ba da karin bayanin shari'a kan takarar da aka yi ba bisa doka ba da ikon wallafa wake-wake da shirye-shiryen TV da dai sauransu don sa kaimi ga aiwatar da manyan tsare-tsare na wadatar da kasa ta hanyar kimiyya da fasaha.(Halima)