A ran 11 ga wata, shugaban babbar kotun kasar Sin Xiao Yang ya bayyana cewa, a bara kutunan kasar Sin suna tsayawa tsayin daka a kan yanke wa masu laifi hukunci haka kuma sun saki mutane fiye da dubu biyu wadanda ba su da laifi.
A gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka shirya a birnin Beijing a ran 11 ga wata, Xiao Yang ya bayar da rahoto game da aikin da babbar kotu ta kasar Sin ta yi. Malam Xiao ya ce, a bana, kotunan kasar Sin za su ci gaba da tabbatar da hakkin 'dan Adam a fannin shari'a da kuma tsara da kyautata tsarin shaida domin hana kuskure da aka yi a yayin da ake shake hunkunci.(Danladi)
|