Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-11 18:05:31    
Wakilan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin sun karyatad da zargin da Amurka ta yi wa kasar Sin ba gaira ba dalili a kan hakkin bil-Adama

cri
A ran 10 ga wata, wakilai daga bangaren watsa labarai da na madaba'a wadanda a halin yanzu ke halartar taron shekara shekara na majalisar ba da shawara a kan harkokin siyasa ta kasar Sin a nan birnin Beijing, sun karyatar da zargin da kasar Amurka ta yi wa kasar Sin ba gaira ba dalili a kan halin da take ciki a fannin hakkin bil Adama a cikin rahoton hakkin bil Adama na kasa da kasa na shekara ta 2005 da ta bayar kwanan baya.

Wani wakili mai suna Zhao Qizheng ya ce, a bayyane ne aka tanadi girmama da kuma tabbatar da hakkin bil Adama na dukan jama'a a cikin tsarin mulkin kasar Sin, kuma kasar Sin tana ta kara samun ci gaba a fannin harkokin hakkin bil Adama. Akasarin jama'ar kasar Sin suna jin dadin ci gaban, yawancin kasashen duniya ma sun nuna amincewa ga batun. Ya ce, majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta ba da rahoton hakkin bil-Adama don tsoma baki cikin harkokin hakkin bil-Adama na kasashe daban daban, amma duk da haka, ba ta rubuta nata a ciki.

Wakilan suna ganin cewa, a cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta tsaya tsayin daka a kan tuhumar al'amuran keta hakkin bil Adama, kuma halin da take ciki a fannin hakkin bil Adama ma ya kara kyautatuwa sosai.(Lubabatu Lei)