Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-11 17:17:51    
Wakilai da mambobi na taruruka biyu na kasar Sin sun yi jawabai yadda suka ga dama

cri

Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin suna nan suna yin taron shekara shekara a nan birnin Beijing, kafofin watsa labaru na kasashen yamma sun bayar da labarai da yawa a kan shawarwari da shirye-shiryen kudurai da wakilai ko mambobi suka bayar, labaran da suka bayar sun zama shaidu ga jawaban da wakilai ko mambobi suka yi yadda suka ga dama.

Batutuwa masu jawo hankulan mutane da wakilai ko mambobin majalisu biyu suka bayyana wajen ayyukan gina sabbin kauyuka da yin adawa da neman 'yancin Taiwan da yaki da cin hanci da rashawa da aikin likitanci da kiwon lafiya da shirya wasannin Olimpic cikin tsimi da dai sauransu dukkan sun zama abubuwan da kafofin watsa labaru na kasashen waje suka yi amfani da su a cikin labarunsu nay au da kullum. Bisa kallon da aka yi ba sosai ba, a cikin lokacin da bai cika mako guda da aka yi bikin budewar tarurukan biyu , yawan labaran da kamfanin dillancin labaru na AP da na Reuters da na AFP suka bayar dangane da shawarwari da shirye-shiryen kuduran da mambobi ko wakilai suka gabatar ya kai 20 zuwa 30.(Halima)