Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-11 17:09:26    
Masu sauraron gidan rediyon kasar Sin suna lura da tarurrukan majalisun kasar Sin biyu

cri
Yanzu, ana yin taro na hudu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 10 da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin ta 10 a nan birnin Beijing. Gidan rediyo kasar Sin ya aika da takardu zuwa ga masu sauraro da masu karatun tashar Internet dinsa dubu 200 na kasashe sama da 160 na nahiyoyi biyar don binciko ra'ayoyinsu kan wadannan tarurruka biyu. Daga binciken nan da aka yi, an gano cewa, yawancin masu sauraronmu da masu karatunmu suna mai da hankali sosai ga manyan batutuwa da ake tattaunawa a kan yadda gwamnatin Sin za ta sassauta nauyi da ke bisa wuyan manoma, ta soke kudin makarata da ake biya kwata kwata yayin da ake bai wa yara ilmin tilas, kuma za ta fara aiwatar da sabon shirin shekaru biyar na raya kasar Sin a nan gaba kadan.

A cikin takardarta, mai sauraro Madam Kala Trital Bhattarai ta kasar Nepal ta ce, "yayin da firayim ministan kasar Sin ke gabatar da rahoto kan ayyukan gwamnati a gun taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin za ta yi iyakacin kokari wajen gaggauta raya kauyuka, ta tabbatar wa manoma ikonsu da kuma moriyarsu. Kasar Sin wata babbar kasa ce a fannin aikin gona, yawan mutane da ke zama a kauyukanta ya wuce miliyan 800. Kullum kasar Sin tana daukar matakai daban daban wajen gaggauta bunkasa aikin gona da raya kauyuka. Kasar Nepal ma wata kasar noma ce. Ya kamata, kasar Nepal ta yi koyi da kyakkyawan sakamako mai yawa da kasar Sin ta samu wajen bunkasa aikin gona. "

Mai sauraronmu Helder Paulo Silva dan kasar Brazil ne wanda ke da shekaru 19 da haihuwa a bana. Bisa matsayinsa na dan makaranta ya nuna babban yabo ga matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka don soke duk kudin marakanta da ake biya a kauyukan kasar, yayin da ake bai wa yara ilmin tilas. Yana ganin cewa, "wannan wani muhimmin al'amari ne ga tarihin kasar Sin dangane da bunkasa aikin ba da ilmi. Manoma matalauta za su iya amfani da kudin makaranta da suke biyawa a da wajen sayen abubuwan zaman yau da kullum. Haka nan kuma idan wata kasa ta iya samun bunkasuwa da ci gaba, to, wajibi ne, ta dogara da aikin ba da ilmi. Matakin nan zai tabbatar da ba da kyakkyawan ilmin tilas ga yaran duk kabilu na wurare daban daban har cikin shekaru 9. Haka zalika mai yiwuwa ne, yaran nan za su sami damar shiga babbar makarantar sakandare da jami'i, sa'an nan kasar Sin za ta kara samun kwararru masu yawa."

Taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ake yi a wannan gami zai dudduba shirin shekaru biyar na bunkasa tattalin arzikin kasa da zaman jama'a da majalisar gudanarwa ta tsara. Da Malam Gilbert Van Kerckhove, kwararren masana'antu na kungiyar 'yan kasuwa ta kungiyar hadin kan Turai wato EU a kasar Sin ya tabo magana a kan wannan shiri, sai ya ce, yana fatan shirin nan zai kara mai da hankali ga masana'antu madaidaita da kanana na kasar Sin, ya kimanta cewa, nan gaba 'yan kasuwa na kasashen waje za su nuna himma ga zuba wa masana'antu madaidaita da kanana kudaden jari.

Bisa binciken da gidan rediyonmu ya yi, an ce, kashi 80 cikin dari na masu sauraronmu da masu karatunmu sun bayyana cewa, dinkuwar kasar Sin gu daya burin jama'a ne. Malam Dong Dezi, mai sauroronmu na kasar Amurka ya bayyana cewa, "mun yi Allah wadai da surutun banza da Chen Shuibian, shugaban hukumar Taiwan ya yi a kwanakin nan kan kara namen "'yancin kan Taiwan", muna nuna goyon bayanmu ga duk matakai da kasar Sin za ta dauka don yin adawa da 'yan a-ware."

Jama'a masu sauraro, nan da kwanaki masu zuwa, gidan rediyo kasar Sin zai ci gaba da watsa muku labaru a kan wadannan tarurrukan majalisun kasar Sin biyu da ake yi a  nan birnin Beijing cikin lokaci. (Halilu)