Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-11 16:30:49    
Kawancen kasashen Afrika ya shirya taro kan batun kare zaman lafiya a yankin Darfur

cri
Majalisar kula da harkokin zaman lafiya da kwanciyar hankali ta kawancen kasashen Afrika ya shirya taron ministoci a birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha a ran 10 ga wata, don yin tattaunawa a kan batun cewa, ko kawancen kasashen Afrika zai mika aikin kare zama lafiyar yankin Darfur na kasar Sudan ga rundunar sojoji na sauran kasashe ko a'a.

Yankin Darfur yana yammacin kasar Sudan. Tun bayan da kungiyar Liberation Movement ta kasar Sudan da kungiyar Justice and Equality da kuma sauran kungiyoyin mutanen yankin suka fara daukar matakan soja wajen yin adawa da gwamnati a farkon shekarar 2003, an yi hasarar rayukan mutane sama da dubu 10, sa'an nan kuma mutane sama da miliyan 2 sun rasa muhallansu. Bisa sulhuntawar da gamayyar kasa da kasa wadda kawancen kasashen Afrika ke ginshikinta suka yi, gwamnatin kasar Sudan da dakaru masu adawa da gwamnati sun daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakaninsu a watan Afrilu na shekarar bariya. Bayan haka rukuni na farko na sojojin kare zaman lafiya da kawancen kasashen Afrika ta aika sun isa yankin Darfur a watan Augusta na shekarar bariya, sun fara aiwatar da aikinsu na kare zaman lafiya. Ya zuwa yanzu dai, yawan sojojin kawacen kasashen Afrika da aka girke a yankin nan ya karu zuwa sama da 7000.

Sojojin kawancen kasashern Afrika sun taka muhimmiyar rawa wajen sanya ido a kan yadda bangarori biyu masu fattatawa da juna suke aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kare kwanciyar hankali a yankin, amma sun gamu da wahalhalu masu yawa. A farkon shekarar nan, majalisar kula da harkokin zaman lafiya da kwanciyar hankali ta kawancen kasashen Afrika ta shelanta cewa, tana nuna goyon baya ga ci gaba da girke sojojin kawancen kasashen Afrika a yankin har zuwa karshen watan Maris na bana bisa yarjejeniyar da aka daddale, bayan wannan lokaci kuma za ta mika aikin karen zaman lafiyar yankin Darfur ga majalisar dinkin duniya.

Kofi Annan, babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bayyana a kan wannan cewa, majalisar dinkin duniya tana son sauke wannan aiki da ke bisa wuyanta. Sa'an nan sakatariyar majalisar dinkin duniya ta tsara shirin girke sojojin kare zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a yankin Darfur na kasar Sudan. Amma kasar Amurka ta nuna ra'ayinta sosai cewa, a aika da sojojin kare zaman lafiya na kungiyar tsaro ta NATO da majalisar dinkin duniya zuwa yankin Darfur. Bangaren Sudan ya nuna kiyewa mai zafi ga ra'ayoyin nan da kasar Amurka da majalisar dinkin duniya suka nuna.

A ran 22 ga watan jiya, Majalisar dokoki ta kasar Sudan ta shirya taron musamman domin yin tattaunawa kan batun girke sojojin kiyaye zaman alfiya na kasa da kasa a yankin Darfur, kuma ta yanke shawara a kan kin amincewa da duk nufin mika aikin sojojin kawancen kasashen Afrika ga sojojin kasa da kasa na majalisar dinkin duniya, haka nan ta yi adawa da duk tsoma hannu da kasashen waje ke yi cikin harkokin gida na kasar Sudan ta ko wace hanya. Hukumar sojojin kasar Sudan ta bayyana cewa, rundunar sojojin Sudan sun riga sun kasance cikin shiri don yin dagiya da mahara na kasashen waje. Mutane dubbai na birnin Khartoum, hedkwatar kasar Sudan sun runtuma a kan tituna don yin zanga-zanga a ran 8 ga wata don nuna kiyewa ga mika wa majalisar dinkin duniya aikin kare zaman lafiyar Darfur daga hannun kawancen kasashen Afrika, kuma sun yi adawa da tsoma hannu da kasashen waje ke yi cikin harkokin gida na kasar Sudan.

Kafofin watsa labaru suna ganin cewa, mai yiwuwa ne, gwamnatin kasar Sudan za ta canja matsayinta a kan batun Darfur, amma abin gaggawa da ake bukata a yi a yanzu, shi ne samun babban ci gaba wajen gudanar da aikin kare zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan. (Halilu)