A ran 8 ga wannan wata (agogon Amurka), majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta bayar da wani rahoto dangane da halin da kasashe daban daban suke ciki wajen hakkin dan Adam a shekarar 2005. A cikin rahoton, Amurka ta sa baki da ta ga dama a kan halin da kasashe da jihohi 190 ko fiye suke ciki wajen hakkin dan Adam, amma ba ta ce kome ba a kan batunta na keta hakkin dan Adam cikin tsanani sosai. Game da wannan, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da bayyanai dangane da hakkin dan Adam na ksar Amurka a shekarar 2005 nan da nan, wannan ya bayyana halin da kasar Amurka take ciki na keta hakkin dan Adam a shekarar da ta shige daga dukan fannoni. Kwararrun hakin dan Adam na kasar Sin su ma suna ganin cewa, ya kamata gwamnatin Amurka ta mai da hankali ga batun kasarta na kanta dangane da hakkin dan Adam.
Rahoton da majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta bayar dangane da halin da kasashe daban daban suke ciki na keta hakkin dan Adam ya ba da sharhi a kan halin da kasashe da jihohi fiye da 190 suke ciki dangane da hakkin dan Adam, amma ba ta leka batun da ke kasancewa a kasarta na keta hakkin dan Adam cikin tsanani sosai ba, a wajen sashen kasar Sin, ta yi biris da hakikanin abubuwan da ke kasancewa a kasar, ta rikitar da halin da kasar take ciki dangane da hakkin dan Adam da kuma kai suka gare ta kiri da muzu.
Shehun malami kuma mai binciken hakkin dan Adam na kasar Sin yana ganin cewa, kullum kasar Amurka tana aiwatar da ma'aunoni iri biyu a kan batun hakkin dan Adam, tana yin wannan ne domin moriyarta ta kanta kawai. Ya bayyana cewa, batun hakkin dan Adam wani muhimmin kayan da kasar Amurka take amfani da shi ne don kara habaka karfinta a kasashen waje da kuma yada tsarin wayin kai na wai kasashen Yamma, kuma ya taba ba da gudumuwa wajen wargaze kasashen Turai ta gabas da tsohuwar tarayyar Soviet, shi ya sa a yau kuma tana ci gaba da yin amfani da irin wannan makami don sa ido na wai kan halin da kasashe da jihohi fiye da 100 na duniya suke ciki wajen hakkin dan Adam a kowace shekara, duk ayyukan da ta yi don ganin cewa, ko ka dace da bukatun kasar Amurka da ma'auninta, idan ba a dace da nata ba, to za ta kai suka da zargi gare ka.
Game da rahoton nan na kowace shekara, a cikin shekaru 7 a jere ne, ofishin watsa labaru na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da bayanai kan halin da kasar Amurka take ciki dangane da hakkin Dan Adam. Bayanin da ofishin nan na kasar Sin ya bayar dangane da hakkin dan Adam na kasar Amurka ya ba da abubuwa masu yawan gaske don bayyana halin da kasar Amurka take ciki na matukar keta hakkin Dan Adam . Shehun malami Liu Wenzong ya bayyana cewa, bayanin ya mai da hankali ga rubuta yadda Amurkawa suke zaman rayuwa da lafiyar jikinsu, Mr Liu ya bayyana cewa, game da halin da kasar Amurka take ciki wajen hakkin dan Adam, batu mafi muhimmanci shi ne yin laifin nuna karfin tuwo mai tsanani sosai, a kowace shekara, kwatankwacin yawan al'amuran da ke sa mutane kashe kansu da kuma laifufukan kisan kai da aka yi wa sauran mutane ya kai dubu 50, a shekarar 2004, yawan laifufukan da aka yi da karfin tuwo a kasar Amurka ya kai miliyan 5.18, daga mutane 47 na kasar Amurka, da akwai mutum daya da ya sha lahani daga wajen laifin nuna karfin tuwo.
Mr Liu Wenzong ya ci gaba da bayyana cewa, daga hakikanin abubuwan da suka faru a kasar Amurka, ana iya ganin cewa, ksar Amurka ba kasa ce da ke da hakkin dan Adam sosai da sosai ba, ya bayyana cewa, a ganina, ya kamata kasar Amurka ta maid a hankali ga halin da take ciki wajen hakkin Dan Adam, kuma ta dauki hakikanin mataki don kyautata halinta na hakkin Dan Adam, ba ta cancanci kai suka ga sauran kasashe ba.(Halima)
|