Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-09 17:39:46    
Zhou Peiyuan, mai aza harsashin ilmin kere-kere na zamani na kusa-kusa na kasar Sin

cri

Marigayi Zhou Peiyuan shi shahararren masanin ilmin kere- kere da ilmin yanayin hallitu da aikin ba da ilmi da aikace-aikacen zaman al'umma na kasar Sin ne. Kuma shi dan J.K.S. ne kuma dan cibiyar binciken kimiyya ta kasar, kuma wanda ya aza harsashin ilmin kere-kere na zamani na kusa-kusa, kuma daya daga cikin masu aza harsashin ilmin yanayin hallitu na kasar Sin.

An haifi Mr. Zhou Peiyuan ne a watan Agusta na shekarar 1902 a birnin Yixin na lardin Jiangsu. A shekarar 1924 ya gama karatu daga makarantar Qinghua wato tsohuwar jami'ar Qinghua, daga baya kuma ya je kasar Amurka don yin dalibta a can, a shekarar 1928 ya sami digiri na dokta wato digiri na 3 na ilmin yanayin halittu na kolejin yanayin halittu ta jihar California ta Amurka, a wannan shekara kuma ya je kasar Jamus don yin binciken ilmin kere-kere cikin jami'ar Leipzig ta kasar Jamus.

Bayan da ya dawo kasar Sin a shekarar 1929, bi da bi ne ya taba zama farfesa a jami'ar Qinghua da hadaddiyar jami'ar kudu maso yammacin kasar Sin da kuma jami'ar Beijing.

Bayan samun 'yancin kasar Sin, Mr. Zhou Peiyuan ya taba zama shugaban kula da harkokin koyarwa na jami'ar Qinghua da shugaban jami'ar Beijing, da mataimakin shugaban cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin da ta duk duniya, da mataimakin shugaban direktan kungiyar ilmin kere-kere ta kasar Sin, da shugaban kungiyar Jiusan. Kuma ya taba zama mamban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da mamban zaunannen kwamitin na majalisar ba da shawara ta jama'ar kasar Sin. A shekarar 1980, ya sami digiri na doktan girmamawa na ilmin shari'a na jami'ar Princeton ta Amurka, a shekarar 1980 da ta 1985 kuma ya sami yabon "abokin jami'a mai ba da fifitaccen taimako" na kolejin yanayin halittu ta jihar California ta Amurka har sau 2.

Nasarar da Mr. Zhou Peiyuan ya samu wajen ilmi ta bayyanu musamman a fannoni 2 na hasashen yanayin halittu, wato binciken da ya yi wajen ilmin kere-kere. Mr. Zhou ya dukufa kan aikin ba da ilmi na jami'a har na tsawon fiye da shekaru 60, dalibansa sun barbazu ko'ina a kasar Sin da kasashen waje, daga cikin su har da shahararrun masanan kimiyya. Mr. Zhou yana da kayyatacciyar fasaha wajen ba da darasi da tafiyar da harkokin makaranta, har ya haifar da masa halayyar kansa wajen ba da ilmi da horar da dalibai da tunaninsa wajen tafiyar da harkokin makaranta, sabo da zurfin ilminsa da ra'ayoyinsa da kuma dabarunsa wajen koyar da dalibai, shi ya sa aka lakaba masa da sunan "wani babban malami wanda ya ke da dalibai ko'ina a duniya."

Bisa matsayisa na fifitaccen dan siyasa, Mr. Zhou Peiyuan ya himmantu ga yin mu'amala tsakanin kasashen duniya wajen kimiyya da fasaha, da yin kokarin neman kwance damara da shimfida zaman lafiya a duk duniya, ya yi matukar kokari kuma ba tare da kasala ba domin kyautata sha'anin kimiyya da fasaha da aikin ba da ilmi na kasar Sin, sabo da haka ya sami girmamawa daga wajen mutane masu binciken kimiyya da fasaha, mutane suna masa yabo cewa, shi mai ba da misalin koyo ne ga masanan kimiyya, kuma shi "tsoho ne mai shimfida zaman lafiya" da "fifitaccen dan diplomasiya mai zaman kansa." (Umaru)