Bayan wucewar ranar babbar sallar gargajiya ta jama'ar Sin wato Spring Festival a Turance da aka yi ba dadewa ba a shekarar nan, sai gwamnatin kasar Sin ta bayar da cikakkiyar takardar bayaninta ta farko wadda babban takenta shi ne "raya kauyukan gurguzu irin na sabon solo ". Ga shi yanzu kuma ana mai da hankali sosai ga tattauna batun raya kauyuka na sabon salo a gun tarurrukan shekarar nan da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin ke yi a nan birnin Beijing.
Malam Qiao Zhanshan, dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wanda ya fito daga karkarar birnin Yan'an da ke a arewa maso yammacin kasar Sin, ya yi shekaru sama da 30 a matsayin jami'in kauyensa, ya bayyana irin kauyuka na sabon salo da ke cikin zuciyarsa. Ya ce, "kudin shiga da manoma ke samu ya karu, wuraren kwanansu ya sami kyautatuwa, an kayatar da kauyukansu, matsayin ilminsu ma ya dagu. Hukumomin kauyuka suna kula da harkokin kauyuka ta hanyar dimokuradiyya. Bayan da aka gama aikin gina kauyukan gurguzu iri na sabon salo, manoma za su jin dadin zaman rayuwarsu kwarai."
Wannan buri daya ne ga manoman kasar Sin da yawansu ya wuce miliyan 900. A halin yanzu, kauyukan kasar Sin suna baya baya idan an kwatanta su da birane a kasar Sin. Matsakaicin yawan kudin shiga da ko wane manomi ke samu ya yi kasa da na dan birni nesa ba kusa ba. Manoma da yawa ba su da kudin ganin likita, kuma ba su da kudin sanya yaransu cikin makaranta. Wani manomi mai suna Zheng Benli na lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin ya bayyana burinsa a manyan fannoni uku. Ya ce, "na farko, za a yi aikin noma ta hanyar zamani don kara girbin hatsi mai armashi; na biyu, kungiyoyi masu hidimar aikin noma za su yi wa manoma hidima a kauyuka da filayen gona. Na uku kuma yana fatan za a kafa wata babbar cibiyar al'adu a kauyensa don koyon fasahar aikin gona da tsarin dokoki don kare moriyarsu."
Manoma suna fatan kara samun girbin amfanin goma mai armashi, a tsabce kauyukansu, kuma su kara nakaltar ilmi mai yawa. Irin wannan burinsu ya samu babban goyon baya daga wajen wakilai mahalartan tarurruka na majalisun nan biyu na kasar Sin. Malam Chen Yaobang, wakilin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin wanda ya taba rike mukamin ministan aikin gona na kasar yana ganin cewa, za a raya kauyuka irin na sabon salo a fannoni da dama. Ya ce, "abin da ake nufi da kauyuka na sabon salo shi ne a bunkasa tattalin arziki wato raya aikin gona na zamani, kuma a kara inganta manyan ayyuka, wannan yana da matukar muhimmanci ga yalwata aikin gona ta hanyar zamani da kyautata zaman rayuwar manoma. Ban da wadannan kuma ya kamata a bunkasa harkokin al'adu da na ba da ilmi da magunguna da wasannin motsa jiki da makamantansu. Haka zalika a bunkasa harkokin siyasa a kauyuka, wato a gudanar da harkokin hukumomin kauyuka ta hanyar dimokuradiyya. "
A cikin rahotonsa kan ayyukan gwamnati na shekarar nan, firayim minista Wen Jiabao ya nanata cewa, ya kamata, gwamnati ta gaggauta raya kauyuka na sabon salo, kuma za ta dauki matakai masu muhimmanci da dama. Ya ce, "bisa kasafin kudinta, gwamnatin kasar Sin za ta kashe kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 339.7 domin aikin gona da kauyuka da manoma a shekarar nan, wato ke nan ya karu da kudin Sin Yuan biliyan 42.2 bisa na shekarar bara. Za a kara wa manoma kudin shiga mai yawa ta hanyoyi daban daban, za a kafa kyakkyawan tsarin zuba jari cikin zaman karko, ta yadda za a sami kyautatuwa sosai wajen yin manyan ayyuka a kauyuka. Haka zalika an soke haraji kwata kwata da aka buga a kan aikin gona a duk kasa tun daga shekarar nan don manoma su sami fa'ida. (Halilu)
|