Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-09 16:29:52    
Wakilan jama'ar majalisar kasar Sin suna mai da hankalinsu kan bunkasuwar sha'anin ba da ilmin ayyuka

cri

Yanzu ana yin taron shekera shekara na majalisar wakilan jama'a na kasar Sin. Wen Jiabao firayin ministan kasar Sin ya yi rahoton gwamnatin a taron, ya ce, bunkasa sha'anin da ba ilmin ayyuka wani aiki mai muhimmanci kuma mai gaggawa, a cikin shekaru 5 masu zuwa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin za ta samar da kudi yuan billiyan 10 na RMB don goyon baya sha'anin.

Wannan buri daya ne ga manoman kasar Sin da yawansu ya wuce miliyan 900. A halin yanzu, kauyukan kasar Sin suna baya baya idan an kwatanta su da birane a kasar Sin. Matsakaicin yawan kudin shiga da ko wane manomi ke samu ya yi kasa da na dan birni nesa ba kusa ba. Manoma da yawa ba su da kudin ganin likita, kuma ba su da kudin sanya yaransu cikin makaranta. Wani manomi mai suna Zheng Benli na lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin ya bayyana burinsa a manyan fannoni uku. Ya ce, "na farko, za a yi aikin noma ta hanyar zamani don kara girbin hatsi mai armashi; na biyu, kungiyoyi masu hidimar aikin noma za su yi wa manoma hidima a kauyuka da filayen gona. Na uku kuma yana fatan za a kafa wata babbar cibiyar al'adu a kauyensa don koyon fasahar aikin gona da tsarin dokoki don kare moriyarsu."

Manoma suna fatan kara samun girbin amfanin goma mai armashi, a tsabce kauyukansu, kuma su kara nakaltar ilmi mai yawa. Irin wannan burinsu ya samu babban goyon baya daga wajen wakilai mahalartan tarurruka na majalisun nan biyu na kasar Sin. Malam Chen Yaobang, wakilin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin wanda ya taba rike mukamin ministan aikin gona na kasar yana ganin cewa, za a raya kauyuka irin na sabon salo a fannoni da dama. Ya ce, "abin da ake nufi da kauyuka na sabon salo shi ne a bunkasa tattalin arziki wato raya aikin gona na zamani, kuma a kara inganta manyan ayyuka, wannan yana da matukar muhimmanci ga yalwata aikin gona ta hanyar zamani da kyautata zaman rayuwar manoma. Ban da wadannan kuma ya kamata a bunkasa harkokin al'adu da na ba da ilmi da magunguna da wasannin motsa jiki da makamantansu. Haka zalika a bunkasa harkokin siyasa a kauyuka, wato a gudanar da harkokin hukumomin kauyuka ta hanyar dimokuradiyya. "

gwamnati ta gaggauta raya kauyuka na sabon salo, kuma za ta dauki matakai masu muhimmanci da dama. Ya ce, "bisa kasafin kudinta, gwamnatin kasar Sin za ta kashe kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 339.7 domin aikin gona da kauyuka da manoma a shekarar nan, wato ke nan ya karu da kudin Sin Yuan biliyan 42.2 bisa na shekarar bara. Za a kara wa manoma kudin shiga mai yawa ta hanyoyi daban daban, za a kafa kyakkyawan tsarin zuba jari cikin zaman karko, ta yadda za a sami kyautatuwa sosai wajen yin manyan ayyuka a kauyuka

Wakili Liu Bing daga lardin Jiangxi ya ce, "bunkasa sha'anin ba da ilmin ayyuka batu mai muhimmanci sosai ga kasar Sin, wannan bukatar da duk kokarin zaman al'umma."