Wakilan Hong Kong da na Macao wadanda yanzu ke halartar tarurrukan shekarar nan na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin sun bayyana a birnin Beijing a kwanakin nan cewa, Hong Kong da Macao za su sami damar harkokin kasuwanci mai yawa daga sabon shirin shekaru biyar na bunkasa tattalin arzikin kasar Sin da zaman jama'arta don bunkasa tattalin arzikinsu.
Malam Yang Sunxi, wakili a zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin kuma shugaban rukunin Heung Kong na Hong Kong ya bayyana cewa, abubuwa da aka tanada cikin wannan daftarin tsarin ka'idojin shirin nan dangane da Hong Kong da Macao gwarin guiwa ne da aka yi wa bangaren masana'antu da na kasuwanci na Hong Kong. Haka zalika abubuwa da yawa da suka shafi aikin raya babban yankin kasar Sin su ma za su kawo fa'ida sosai ga tattalin arzikin Hong Kong.
Wakilan nan na Hong Kong da Macaco suna ganin cewa, bisa abubuwa da aka tana a cikin daftarin tsarin nan, an karfafa magana musamman a kan hadin guiwa da ma'amala da ake yi tsakanin babban yankin kasar Sin da Hong Kong da Macao. Wannan zai kara karfin hadin kai a tsakaninsu, ta yadda za su sami bunkasuwa tare. (Halilu)
|