Mataimakin ministan kudi na kasar Sin, Zhu Zhigang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi ta kara zuba jari ga kauyuka da kuma a wajen ayyukan noma, ta yadda manoma za su kara jin dadin sakamakon da aka samu daga bunkasuwar kasar da kuma gyare-gyaren da aka yi a kasar.
Ya ce, a shekarar da muke ciki, kasar Sin za ta soke harajin da aka buga a kan ayyukan noma daga dukan fannoni, kuma za ta ci gaba da kyautata tsarin kudin taimako da aka bai wa manoma don sa kaimi gare su da su shuka hatsi, haka kuma kasar Sin za ta kara zuba jari a wajen ba da ilmin tilas a kauyuka, kuma za ta fara soke kudin makarantar firamare da na sakandare a yammacin kasar, bayan haka, za ta kuma kara zuba jari don warware matsalolin da manoma suke sha a wajen ganin likita.(Lubabatu Lei)
|