Zaunannen wakilin Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin kuma shahararren marubuci Mr. Wang Meng ya yi kira a nan Beijing a ran 8 ga wata, ga 'yan uwa na gabobi 2 da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan da su yi kokari tare wajen nuna kiyewa da hana yunkurin 'yan-a-ware na neman samun 'yancin kan Taiwan, ta yadda za a raya dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan cikin jituwa.
Mr. Wang ya yi wannan bayani ne a gun taron ganawa da manema labaru da taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ya shirya. Ya kara da cewa, bangaren babban yankin kasar Sin yana fatan za a raya dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan cikin jituwa, shi ya yi cudanya da mu'amala mai jituwa tare da takwarorinsa na Taiwan. Amma yunkurin 'yan-a-ware na neman samun 'yancin Taiwan ya kawo wa dangantakar da ke tsakanin gabobin nan 2 illa, kuma zai kawo hadari.(Tasallah)
|