Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-08 16:10:54    
Wane irin ma'anar bunkasuwa da kasar Sin ta yi wa duniya ?

cri

A kwanan nan, birnin Beijing ya zama wurin da duk duniya ke mai da hankali gare shi , duk saboda mutane fiye da dubu 5 da suka zo daga wurare daban daban na kasar Sin sun taru gu daya a wurin, kuma a madadin mutanen kasar Sin da yawansu ya kai mil iyan 130 ne suka yi tattaunawa kan yadda kasar Sin za ta sami bunkasuwa a nan gaba, da kuma yi duddubawa kan rahoton da aka yi  kan ayyukan gwamnati . A cikin shekaru 27 da suka wuce, tattalin arzikin kasar Sin ya sami bunkasuwa da saurin gaske, kuma karfin kasa ya kara daguwa a bayyane. Bisa tsammanin da ake yi yanzu, an ce, a cikin shekaru 15 masu zuwa, yawan tattalin arzikin kasar Sin shi ma zai kara karuwa da ninki biyu. Amma mun ji ra'ayoyi da suka nuna cewa, wai kasar Sin kalubale ne, kuma ra'ayoyin nan na da bambance bambance, daga kalubalen da ya zo daga hatsi zuwa kalubalen da ya zo daga makamashi, sa'anan kuma daga kalubalen masana'antu zuwa kalubalen soja, kai, wane irin ma'anar bunkasuwa da kasar Sin wadda ke samun karuwa da saurin gaske cikin zaman karko ta kawo wa duk duniya?

Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana a cikin rahotonsa a ran 5 ga wannan wata cewa, za mu ci gaba da bin hanyar raya kasa cikin lumana ba tare da kasala ba. A cikin harkokin kasa da kasa, mu nace ga bin dimokuradiya da adalci , kuma a sa kaimi ga yin hadin guiwa bisa adalci da kuma nacewa ga samun jituwa da amincewar juna da ci gaba da yin tsaron kai gaba daya da nacewa ga bin zaman daidaici da samun moriyar juna da sa kaimi ga samun wadatuwa gaba daya, a nace ga bude wa kasashen waje kofa da sa kaimi ga yin shawarwari cikin wayin kai ,kuma cikin himma da kwazo ne za a sa kaimi ga raya tsarin kasa da kasa bisa dacewa da adalci.

A wajen harkokin siyasa da tsaron kai, da batun nukiliyar Zirin tekun Korea da aikin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da kuma hana yaduwar makaman nukiliya a kasashen duniya, maganar da kasar Sin ta kan yi shi ne, sa kaimi ga samun zaman lafiya, kada a yi fadace da fadace. Kakakin kawancen kasashen Turai mai kula da huldar waje malama Edwen ta amince da cewa, na lura da maganganun da shugabannin kasar Sin suka yi a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, daga cikinsu, ana iya ganin niyyar da kasar Sin take yi don neman samun bunkasuwa cikin lumana. A bayyane ne, kasar Sin tana nan tana sa kaimi ga shimfida zaman lafiya a shiyya shiyya. Mun amince cewa, kasar Sin tana kokarin cim ma burinta na samun bunkasuwa cikin lumana da kuma neman hadin guiwar da za a yi da ita.

A wajen harkokin tattalin arziki da cinikayya da kasar Sin take yi da kasashen waje, da farko, a kasashen kudu maso gabashin Asiya, an yi jita jita cewa, wai kasar Sin ce ta iya kawo kalubale , amma abubuwan da suka faru a cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce sun shaida cewa, bayan bunkasuwar kasar Sin, kasar Sin ta riga ta zama mai jagorancin raya tattalin arzikin kungiyar Asean, wato kungiyar ta sami fa'ida ta hakika, kuma bangarorin nan biyu suna yin cinikayya cikin 'yanci. A wannan lokaci, in an ce wai kasar Sin ta kawo kalubale, sai kungiyar ta gaskanta ra'ayin nan domin ba da taimako ga kasar Sin , wani mai bincike na kasar Shingapore mai suna Sheng Lijun ya bayyana cewa, kasar Sin ta samar wa kungiyar Asean fa'ida mai kyau, shi ya sa kasashen da ke cikin kungiyar suka riga suka gyara ra'ayoyinsu da cewar wai kasar Sin ta kawo kalubale.

Jakadan kasar Benin ya bayyana cewa, kullum kasar Sin tana bin hanyarta ta samun bunkasuwa cikin lumana, kuma tana ganin halin da ake ciki a duniya a hankali da kuma aiwatar da manufar harkokin waje ta zaman lafiya, jama'ar Afrika suna girmama kasar Sin sosai.(Halima)