Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-07 19:29:32    
Kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwar moriyar juna da kasashe masu tasowa

cri
A gun taron ganawa da manema labaru da aka yi a nan Beijing a ran 7 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Mr. Li Zhaoxing ya bayyana cewa, kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwar moriyar juna da dukan kasashe masu tasowa don neman samun bunkasuwa tare.

Mr. Li ya bayyana cewa, kasar Sin tana daya daga cikin kasashe masu tasowa, tana da moriyar bai daya da sauran kasashe masu tasowa, kara yin hadin gwiwa da hadin kai da su tushe ne na manufofin kasar Sin a fannin diplomasiyya, har abada kasar Sin za ta ci gaba da son rike huldar abokantaka a tsakaninta da kasashe masu tasowa, da girmama da taimakawa juna da kuma girmama hanyoyin bunkasuwar da suka zaba da kansu bisa halin da suke ciki.(Tasallah)