Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-07 17:53:52    
Sinawa da ke zaune a kasashen waje sun kai suka sosai ga danyen aiki da Chen Shuibian ya yi na neman 'yancin Taiwan

cri

A 'yan kwanakin baya, rukunonin Sinawa da ke zama a kasashen waje sun ci gaba da yin taron tattaunawa da bayar da sanarwa don kai suka mai zafi ga danyen aiki da Chen Shuibian ya yi na neman 'yancin Taiwan, kuma sun bayyana cewa, suna tsayawa tsayin daka don nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Sin dangane da ra'ayinta na siyasa a kan huldar da ke tsakanin bangarorin biyu na zirin tekun Taiwan, sa'an nan kuma suna tsayawa tsayin daka don nuna kiyewa ga rukunin 'yan neman 'yancin Taiwan na kawo baraka ga kasa.

A 'yan kwanakin baya, Sinawa da ke zama a birnin Torino na kasar Italiya sun yi taron tattaunawa, inda suka kai suka mai tsanani a kan shawarar da Chen Shuibian ya yanke wajen watsi da kwamitin dinkuwar kasa da daina aikin tsarin dinkuwar kasa, wannan ne kalubale mai tsanani da ya yi ga manufar kasar Sin daya tak da kasashen duniya suke amincewa da ita.

Sinawa da ke Hungary da Polland kuma su ma sun shirya irin wannan tarurruka.(Danladi)