Za a shirya wasannin Olympic na karo na 29 a birnin Beijing a shekarar 2008. Kogaito Yoshiki mai shekaru 22 da haihuwa wani dalibi ne da ke karatu a Jami'ar Waseda ta kasar Japan, yanzu kuwa yana yin yawon shakatawa a nan birnin Beijing, da ya tabo magana a kan wasannin Olympic na Beijing, sai ya gaya wa wakilinmu ce, tabbas ne, zai sake zuwa birnin Bejing don kallon wasannin Olympic da za a shirya a shekarar 2008.
Kamfanin yawon shakatawa mai suna "Matasa" na birnin Bejing shi ne ya karbi Kogaito Yoshiki. Malam Li Bin, manajan wannan kamfani ya bayyana ra'ayinsa a kan wasannin Olympic na Beijing cewa, "kamfaninmu zai habaka harkokin yawon shakatawa da yake yi a fannoni daban daban don biya wa masu yawon shakatawa bukatunsu a lokacin wasannin Olympic na Beijing. Alal misali yawan gadaje da kamfaninmu yake da su a hotel-hotel ya kai 200 ne kawai a halin yanzu, amma zai karu zuwa 400 ko 500 a shekarar 2008 bisa shirin da ya tsara. "
A lokacin wasannin Olympic na Beijing, ban da cewar za a kyautata wuraren kwana da zirga-zirga domin masu yawon shakatawa, kuma za a jagoranci masu yawon shakatawa zuwa tsoffafin wurare masu ni'ima don yin yawon shakatawa a nan birnin Beijing a lokacin hutun wasannin. Malam Wang Qing, wani jami'in hukumar kula da yawon shakatawa ta birnin Beijing ya tsara wa masu yawon shakatawa shirye-shirye. Ya ce,
"ban da kallon bikin bude wasannin Olympic da na rufewa da kuma gasanni, masu yawon shakatawa za su iya yin ziyara a Babbar Ganuwa da Fadar Sarkunan Kasar Sin da Dakin Ibada mai suna Tiantan da kabarin sarkunan daular Ming da sauran shahararrun tsoffafin wurare biyu na duniya a lokacin hutun wasannin. Haka zalika masu yawon shakatawa za su iya ziyartar tsoffafin kananan hanyoyi na birnin Beijing da tsoffafin gidajen jama'a, su dandana kayayyakin abincin musamman na Beijing, su yi raye-raye tare da 'yan birnin."
Birnin Beijing wani babban birni ne mai arzikin wuraren yawon shakatawa. Ban da shahararrun tsoffafin wurare na duniya kamar Babbar Ganuwa da Fadar Sarkunan kasar Sin, kuma akwai dakunan nune-nune sama da 130 da wuraren yawon shakatawa sama da 270 a nan birnin Beijing. Haka zalika gine-gine da wuraren al'adu irin na zamani sun yi birjik a birnin Bejing. Sabo da haka ba ma kawai masu yawon shakatawa za su sami damar yin yawon shakatawa a tsoffin wurare masu ni'ima na birnin Beijing ba, har ma za su more idanunsu sabbin manyan gine-gine irin na zamani, su sha daularsu.
Ban da birnin Beijing, masu yawon shakatawa da suka fito daga kasashen waje za su sami damar zuwa karkarar birnin da sauran wurare daban daban na kasar Sin don yin yawon shakatawa a lokacin hutun wasannin Olympic. Malam Zhao Xin, wani manaja na kamfanin yawon shakatawa na kasa da kasa ta Sin ya bayyana a kan wannan cewa, "a lokacin wasannin Olympic na Beijing, kamfaninmu zai aika da manyan bos don daukar masu yawon shakatawa daga birnin Beijing zuwa birnin Shanghai da na Xian da Guilin da Guangzhou da sauran wurare don yin yawon shakatawa. Jagoran yawon shakatawa na kamfaninmu za su bayyana wa baki na kasashen waje abubuwa kan wadannan wuraren yawon shakatawa cikin harsunan waje daban daban ta yadda za su fahimta sosai. "
Bayan da aka shiga shekarar nan, hukumomin yawon shakatawa na birnin Beijing sun riga sun gudanar da harkokinsu sosai wajen yin farfaganda a kan wasannin Olympic na Beijing. Za a kammala aikin gina dakuna da filaye na wasannin Olympic daban daban a birnin Beijing a shekarar nan. Haka zalika za a kammala aikin gina lambun shan isaka na wasannin Olympci a Beijing a shekarar badi. Bayan haka duk masu yawon shakatawa za su sami damar dasa bishiyoyi a kewayen gine-ginen wasannin Olympic don tunawa da wasannin. (Halilu)
|