Mataimakin shugaban hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin, Qiu Xiaohua ya bayyana a ran 7 ga wata a nan birnin Beijing cewa, a shekarar bara, ya kasance da rarar kudin da yawansa ya kai sama da biliyan 97 a wajen kudin shiga na kananan hukumomin kasar Sin, shi ya sa babu gibin kudi a gare su.
Qiu Xiaohua ya yi wannan kalami ne yayin da yake halartar taron manema labaru na taron shekara shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa a ran nan a matsayinsa na dan majalisar. Yayin da yake amsa furucin da kafofin yada labarai na waje suka yi na cewa, akwai babban gibin kudi a kananan hukumomin kasar Sin a shekarun nan biyu, ya ce, bisa dokar kasafin kudi ta kasar Sin, ban da gwamnatin tsakiya, ba za a yarda da kasancewar gibin kudi a kananan hukumomin ba.(Lubabatu Lei)
|