Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-07 12:16:56    
Shugaban kasar Korea ta Kudu ya yi ziyara a kasashen Afirka domin neman makamashi

cri
A ran 6 ga wata, shugaban kasar Korea ta Kudu Roh Mu Hyun ya isa birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar domin fara yin ziyarar aiki a kasar Masar. Ban da wannan kuma, zai kai wa kasashen Nijeriya da Algeria ziyara. Wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Korea ta Kudu ya ziyarci kasashen Afirka. Ra'ayin bainal jama'a sun yi hasashen cewa, tun daga shekarar da muke ciki, shugabanni da jami'an kasar Korea ta Kudu sun ziyarci kasashen Afirka a jere, kuma sun karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka a fannin harkokin waje da tattalin arziki, wanda ya bayyana sauyin manufofin kasar Korea ta Kudu kan harkokin waje. Dalilin da ya sa ta yi haka shi ne sabo da tana so ta shigar da man fetur daga kasashe daban daban.

A ran nan, fadar shugaban kasar Korea ta Kudu ta bayyana cewa, nufin Noh Mu Hyun kan kai wa kasashen Afirka uku ziyara na kwanaki 9 shi ne karfafa dangantakar diplomasiyya da ke tsakanin Korea ta Kudu da wadannan kasashe da kuma hadin gwiwa tsakaninsu kan makamashi da tattalin arziki. Haka kuma wata kungiyar wakilai da ke kunshe da kamfanoni da 'yan kasuwa na Korea ta Kudu da yawan mutanenta ya kai 80 ita ma tana yin ziyara a kasashen tare da Roh Mu Hyun, kungiyar suna mai da hankali a kan makamashi da gine-ginen manyan kayayyaki da kuma kayayyakin da ake aikawa da su kasashen waje.

Har kullum kasar Korea ta Kudu ta kan dora muhimmanci kan raya dangankatar diplomasiyya tsakaninta da kasashen Asiya, kuma ba ta yi cudanya tare da kasashen Afirka ba cikin dogon lokaci. Amma tun bayan karshen shekarar ta ta gabata, kasar Korea ta fara mai da hankali a kan Afirka. A cikin watan Nuwamba na shekarar bara, bankin shigi da fici na Korea ta Kudu ya daddale yejejeniyar hadin kai tare da bankin bunkasuwar Afirka. A farkon watan Janairu na shekarar da muke ciki, ministan harkokin waje na kasar Ban Ki-Moon ya ziyarci kasashen Ghana da Congo Kinshasa. A farkon watan Febrairu, firayim ministan kasar Lee Hae Chan ya kai wa kasashen Afirka ta Kudu da Senegal ziyara. Haka kuma shugaban kasar Roh Mu Hyun yana ziyara a wasu mihimman kasashen Afirka yanzu. Ra'ayin bainal jama'ar Korea ta Kudu ya yi hasashen cewa, dalilin da ya sa aka sami sauye-sauyen manufar Korea ta Kudu kan harkokin waje shi ne sabo da kasar tana yin la'akari a kan fannoni biyu.

A fannin siyasa, tare da karuwar karfin kasar Korea ta Kudu, tana neman taka rawa mafi muhimmanci a cikin harkokin duniya don daga matsayinta a duniya. Kasashen Afirka suna ba da muhimmin tasiri a cikin Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin duniya, kasar Korea ta Kudu tana bukatar hadin gwiwa tare da Afirka kan harkokin duniya. Sabo da haka kasar ta canja manufarta kan harkokin waje tun daga shekarar da muke ciki, tana mai da hankali a kan karfafa dangantakar diplomasiyya tsakaninta da kasashen Afirka da kuma yankin gabas ta tsakiya, ban da wannan kuma ta tsai da kudurin kara ba da taimako ga gwamnatocin kasashen Afirka domin samun yabo daga kasashen Afirka.

A fannin tattalin arziki, kasar Korea ta Kudu tana ganin cewa, kasashen Afirka suna da makamashi da albarkatu masu yawa, kuma ya kasance da boyayyen karfi a kasuwa, shi ya sa kasashen Afirka suna da matsayi mai muhimmanci a duniya. Karfafa dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka da kasar Korea ta Kudu ta yi tana iya tabbatar da samun man fetur da sauran makamashi da albarkatu daga Afirka, haka kuma kamfanonin Korea ta Kudu za su samu sabuwar kasuwa da kuma neman samun ayyukan gina manyan kayayyaki a Afirka.

Sabo da kasar Korea ta Kudu ta iya samun moriyar siyasa da tattalin arziki a Afirka, shi ya sa kafofin watsa labarai na kasar sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta kara ba da taimako ga gwamnatocin kasashen da ke kudancin Sahara da kuma karfafa dangantakar da ke tsakaninta da Afirka domin tabbatar da samun moriya daga kasashen Afirka cikin dogon lokaci.(Kande Gao)