Shugaban kwamitin kula da bunkasuwa da gyare-gyare na kasar Sin, Ma Kai ya bayyana a ran 6 ga wata a nan birnin Beijing cewa, nan da shekaru biyar masu zuwa, jama'ar kasar Sin za su kara jin dadin bunkasuwar kasar.
Ma Kai ya yi wannan kalami ne yayin da yake amsa tambayar da wakilinmu ya yi masa a gun taron manema labaru da aka shirya a ran nan. Ya ce, dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta tsara shirin bunkasuwa a cikin shekaru biyar masu zuwa shi ne don neman raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a, musamman ma domin daidaita batutuwan da suke jibintar moriyar jama'a. Ya tsinkayi cewa, ya zuwa shekara ta 2010, bisa bunkasuwar tattalin arziki, jama'ar kasar Sin za su kara samun kudin shiga a zahiri, kuma zaman rayuwarsu ma zai inganta, muhallin zamansu ma zai kyautatu, rukunonin da ke fama da matsalolin zama ma za su kara samun kulawa daga gwamnati da kuma zaman al'umma baki daya.(Lubabatu Lei)
|