
A kwanakin nan a jere, rukunonin Sinawa da ke zama a kasashen waje da daliban kasar Sin da ke dalibta a kasashen waje sun ci gaba da yin taron tattaunawa da bayar da sanarwa don kai suka mai zafi ga danyen aiki da Chen Shuibian ya yi na neman 'yancin Taiwan, kuma sun bayyana cewa, suna tsayawa tsayin daka don nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Sin dangane da ra'ayinta na siyasa a kan huldar da ke tsakanin bangarorin biyu na zirin tekun Taiwan, sa'anan kuma suna tsayawa tsayin daka don nuna kiyewa ga rukunin 'yan neman 'yancin Taiwan na kawo baraka ga kasa, ko kadan ba za a yarda kowane mutum ya balle Taiwan daga kasar Sin ta kowace hanya ba.
A gun taron tattaunawa da aka shirya, wakilan kwamitin tsakiya na hadadiyyar kungiyar Sinawa 'yan kaka gida ta Korea ta Arewa sun bayyana cewa, Chen Shuibian ya tilasta a yi watsi da kwamitin dinkuwar kasa da daina aikin tsarin dinkuwar kasa, wannan ya bayyana muguwar fuskarsa ta neman 'yancin Taiwan a bayyane. Kuma wannan ne kalubale mai tsanani da ya yi ga babban sha'anin dinkuwar kasa da shimfida zaman lafiya a shiyyar da muke zama, kuma wata hanya ce maras mafita .
Sa'anan kuma Sinawan da ke zma a kasar Britaniya da Japan da Myanma da Danmark da Ukaran da Ekwator da Panama da Seychelles da Shingpore da kuma daliban kasar Sin da ke dalibta a wadannan kasashe su ma sun kai suka sosai ga danyen aikin da Chen Shuibian ya yin a soke kwamitin dinkuwar kasa.(Halima)
|