
Mataimakin darektan kwamitin yin gyare-gyare da raya kasa na kasar Sin Mr. Zhu Zhixin ya bayyana a nan birnin Beijing, a ran 6 ga wata cewa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin za ta kara mai da hankali kan wuraren kananan kabilu da karkara da kuma wurare masu fama da talauci, yayin da za ta zuba kudi da tsara manufofin raya masana'antu a cikin shekaru 5 masu zuwa.
Mr. Zhu ya yi wannan bayani ne a gun taron ganawa da manema labaru da aka yi game da shirin bunkasuwa da kasar Sin ta tsara a cikin shekaru 5 masu zuwa a ran nan. Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakai wajen rage gibin da ke tsakanin wurare daban daban na kasar a fannin ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma sannu a hankali, bisa halin da suke ciki, ta yadda jama'ar kasar da ke wurare daban daban za su iya samun zaman rayuwa bisa matsayi daya sannu a hankali.(Tasallah)
|