Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-06 17:44:42    
Kasar Sin za ta kafa tsarin samar da ayyukan kiwon lafiya mai kyau a kauyukanta

cri

Jama'a maso karantawa, mutane fiye da miliyan 750 suna zama a kauyukan kasar Sin, yawansu ya kai misalin kashi 60 cikin dari bisa jimlar mutanen kasar. Saboda dalilai iri daban daban, ya kasance da babban gibi tsakanin kauyuka da birane a fannin kiwon lafiya a kasar Sin, yadda manoma suka kiyaye lafiyarsu, da kuma yadda suka daidaita matsalolin ganin likita dukansu sun jawo hankalin gwamnatin kasar Sin. A 'yan kwanakin nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da cewa, za ta kafa tsarin samar da ayyukan kiwon lafiya mai kyautatuwa a kauyuka a cikin shekaru 5 masu zuwa.

Halin da kauyukan kasar Sin suke ciki a fannin kiwon lafiya yana baya baya sosai, in an kwatanta da halin da biranen kasar suke ciki. Tsarin kiwon lafiya na al'umma bai samu kyautatuwa ba a kauyukan kasar, injuna da ke asibitoci tsoffi ne kuma suna baya-baya, ana fama da karancin nagartattun ma'aikata masu ilmin kiwon lafiya, ba a biyan bukatun majiyyata manoma. A sa'i daya kuma, manoman kasar Sin sun yi karancin samun tabbaci a fannin kiwon lafiya, a galibi dai sun biya kudi da kansu wajen ganin likita. Amma ba su da kudin shiga da yawa, shi ya sa ba su iya kashe kudi da yawa wajen kiwon lafiya. Idan sun kamu da ciwo mai tsanani, da kyar su biya kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubbai, har ma fiye da dubu goma. Saboda haka, manoma na wasu wuraren kasar Sin ba su je asibiti cikin lokaci ba, kuma ba su da isasshen kudi wajen shawo kan miyagun ciwace-ciwacen da suke fama da su.

Don sassauta matsalar da manoma suke fuskanta wajen ganin likita, gwamnatin kasar Sin ta fara kafa sabon tsarin samar da magani a kauyuka cikin hadin gwiwa tun daga shekara ta 2003. bisa abubuwan da aka tanada cikin wannan sabon tsari, an ce, gwamnatin tsakiya ta kasar da kananan hukummomi na wuraren kasar da kuma manoma sun biya wasu kudade wajen kafa asusun kiwon lafiya, ta yadda aka mayar da kudi ga mamonan da suka shiga wannan asusu, bisa ka'idar yawan kudi da aka tsara. Yanzu an riga an soma aiwatar da sabon tsarin a kauyukan kasar da yawansu ya wuce kashi 30%.

Mr. Ma Shichun, wani manomi ne da ke zama a gundumar Changyang ta lardin Hubei. Ya taba fuskantar babbar matsalar rashin isasshen kudi wajen shawo kan ciwon zuciya. Amma sabon tsarin samar da magani a kauyuka cikin hadin gwiwa ya taimake shi sosai, asusun kiwon lafiya ya mayar da kudi gare shi da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 10, a karshe dai ya warke tare da biyan kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 50. Mr. Ma ya ce, "na biya bashin da na ci da kudin da aka mayar da shi gare ni bisa abubuwan da aka tanada cikin sabon tsarin samar da magani a kauyuka cikin hadin gwiwa, wannan sabon tsari ya warware babbar matsalar da muke fuskanta."

Ban da manoma kuma, sabon tsarin samar da magani a kauyuka cikin hadin gwiwa ya ba da taimako ga asibitoci na kauyuka, ya kara kudaden shigarsu, ta haka asibitocin sun yi amfani da wadannan kudade wajen sayen sabbin injuna da horar da ma'aikata da kuma daga matsayin kiwon lafiya. Mr. Hu Youxu, wani likita ne da ke aiki a asibiti na garin Moshi na gundumar Changyang ta lardin Hubei. ya yi bayani kan wannan da cewa, "a da mun yi wa majiyyata jinya kimanin 6 zuwa 8 a asibiti a ko wace rana, amma yanzu wannan adadi ya karu zuwa 18 ko 20, har ma 30 ko fiye. Manoma sun sami riba a sakamakon sabon tsarin samar da magani a kauyuka cikin hadin gwiwa, haka kuma asibitoci sun sami bunkasuwa a sakamakon haka, bangarori daban daban sun sami riba. "

Saboda ganin sakamako mai kyau da aka samu bayan da aka aiwatar da wannan sabon tsari, tun daga shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin daga ka'idar yawan kudin alawas da take baiwa manoman da suka sa hannu cikin asusun kiwon lafiya, da kuma kara aiwatar da wannan sabon tsari a wurare daban daban sannu a hankali. A galibi dai za a aiwatar da shi a duk kauyukan kasar a cikin shekaru 5 masu zuwa. Ministan kiwon lafiya na kasar Sin Mr. Gao Qiang ya bayyana cewa, "hukumomin kudi na tsakiya da na kananan hukumomi za su kara zuba kudi kan manoman da suka sa hannu cikin sabon tsarin samar da magani a kauyuka cikin hadin gwiwa, za su kuma samar da sharudda masu kyau wajen gina da raya wannan sabon tsari."

Kwanan bayan da suke wuce, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta gabatar da shirin bunkasuwa na shekaru 5 masu zuwa, inda ta yi nuni da cewa, a cikin shekaru 5 masu zuwa, gwamnatin kasar za ta yi amfani da kudin da yawansa ya kai yuan fiye da biliyan 20 wajen gina manyan ayyukan kiwon lafiya a kauyuka.(Tasallah)