A ran 5 ga wannan wata da safe a nan birnin Beijing, hukumar mulkin koli ta kasar Sin wato Majalisar Wakilan Jama'ar Kasar Sin ta yi bikin bude babban taronta na shekara shekara, a madadin gwamnatin tsakiya, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayar da rahoto dangane da aikin gwamnati ga babban taron. Rahoton ya kasu sassa guda uku, wato waiwayi aikin da aka yi a shekarar da ta shige, babbar dawainiyar da za a yi a shekarar da muke ciki da karin bayani kan babban shiri na 11 na shekaru biyar biyar na raya tattalin arzikin kasa da zamantakewar al'umma, sa'anan kuma ya gabatar da tunanin aiki da babbar manufa ta gwamnatin kasar Sin a cikin shekarar da muke ciki da shekaru biyar masu zuwa. Daga cikin dukan rahoton, muhimmin abu shi ne zaman rayuwar jama'a. Rahoton na da kalmomi dubu 20, kuma ya hada da aikin gwamnati na shekarar da ta shige da shirin shekaru biyar. Amma, muhimmin abu shi ne don bayar da shirin aiki na shekarar da muke ciki, wannan ya bayyana sosai cewa, gwamnati ta mai da hankali sosai ga batun da ya kasance a halin yanzu.
A wajen takaita ayyukan da aka yi a shekarar da ta shige, firayim minista Wen Jiabao ya takaita cewa, halin da aka ciki a shekarar 2005 ya bayyana cewa, tattalin arziki ya sami karuwa da saurin gaske, sakamakon da aka samu na da kyau sosai, kuma farashin kayayyaki ya zama a gindinsa, daga adadin da rahoton ya fayyace, ana iya ganin cewa, kudin shiga da mazaunan birane da kauyuka suka samu sai kara karuwa suke yi a bayyane, ya kuma tabbatar da kokarin da gwamnati ta yi a shekarar da ta shige wajen daidaita muhimman batutuwan da suka faru a lokacin da aka aiwatar da harkokin tattalin arziki da sa kaimi cikin himma da kwazo ga daidaita tsarin tattalin arziki da hanyoyin kara karuwarsa, a sa'I daya kuma ya bayyana cewa, ana kara samun wahaloli wajen kara karuwar girbin hatsi da kara wa manoma kudin shiga, jama'a sun kuma gamu da wuya wajen ganin likitoci da kuma kudin makaranta na da tsada har ma halin da ake ciki wajen yin aiki cikin lafiya ya yi tsanani sosai, duk wadannan bai boye su ko kadan ba.
Shirin karuwar tattalin arziki da rahoton ya tsai da a shekarar da muke ciki ya kai kashi 8 cikin dari, a sa'I daya kuma ya gabatar da cewa, ya kamata a rage yawan makamashin da za a yi amfani da shi don kara GDP da kashi 4 cikin dari . Rahoton ya kasa muhimman ayyuka na shekarar da muke ciki sassa guda 8 , ciki har da sa kaimi ga raya sabbin kauyuka da kara karfi ga daidaita tsarin masana'antu da yin tsimin albarkatan halittu da kiyaye muhalli da kuma ci gaba da sa kaimi ga yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa da mai da hankali ga daidaita batutuwa dangane da moriyar jama'a ta hakika, wannan ya bayyana halin musamman da ke da amfani ga manoma da mai da muhimmanci ga ba da ilmi da kawar wahaloli , wannan kuma ya dace da kokarin da gwamnati ta yi wajen aiwatar da harkokin mulki don neman adalci a zamantakewar al'umma da samun bunkasuwa cikin jituwa da dai sauransu , duk wadannan halayen musamman an yi bayyanuwarsu ne a cikin tunanin raya kasar Sin a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Don raya kauyuka masu sabon salo, gwamnati za ta daidaita manufarta ta zuba jari, game da wannan, Mr Wen Jiabao ya bayyana cewa, ya kamata a yi niyyar daidaita manufar zuba jari, ya kamata a mayar da muhimmin aiki na zuba jari ga manyan ayyuka na kasa zuwa ga kauyuka, wannan ne muhimmin aiki na sauyawa.
Sa'annan kuma, Mr Wen Jiabao ya yi alkawarin kara zuba jarin kasa da yawansu ya kai kudin Amurka dolla biliyan 27 ko fiye a shekaru biyar masu zuwa , kuma ya gabatar da wani matakin da ba a taba gabatar da shi ba, ya ce, a duk kauyukan kasar Sin , za a aiwatar da harkokin ba da ilmi a fayu, wannan ne muhimmin aiki da za a yi a tarihin ba da ilmi a kasar Sin, tabbas ne zai ba da zurfaffen tasiri ga kara nagari na jama'ar kasar Sin.
Sa'anan kuma, Wen Jiabao ya gabatar da sauran batutuwa dangane da fannoni da yawa, wakilan da suka zo daga wurare daban daban na kasar Sin za su dudduba da kuma jefa kuri'u a kan rahoton nan.(Halima)
|