Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-06 17:23:59    
Yana nan yana kasancewa da wata hanyar yin cudanya tsakanin gwamnatin kasar Sin da Dalailama

cri
Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr. Re Di ya bayyana a nan birnin Beijing, a ran 6 ga wata cewa, yana nan yana kasancewa da wata hanyar yin cudanya tsakanin gwamnatin kasar Sin da Dalailama. Ya kuma jaddada cewa, dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da Dalai ita ce ta mahaifiya da danta.

Bayan da ya yi tattaunawa kan rahoton ayyuka na gwamnatin kasar a ran nan, a lokacin da yake yin zantawa da manema labaru, Mr. Re Di ya bayyana cewa, har kullum gwamnatin tsakiya ta kasar Sin tana aiwatar da manufofinta domin Dalailama, ba ta canja ko kadan ba, wato idan Dalailama ya yi watsi da neman samun 'yancin kai, kuma zai kiyaye dinkuwar kasar Sin gaba daya. Yana nan yana kasancewa da wata hanyar yin cudanya tsakanin gwamnatin kasar Sin da Dalailama. Huldar da ke tsakanin Dalailama da kasar Sin hulda ce ta gida, saboda Dalai dan kasar Sin ne, shi ya sa, huldar da ke tsakaninsu ita ce ta mahaifiya da danta.(Tasallah)