A ran 6 ga wata a birnin Beijing, wakilan da suke halartar taron shekara-shekara na kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka shirya sun dudduba rahoton gwamnatin da aka bayar tare da dudduba shiri na 11 na shekaru 5 na kasar Sin wajen bunkasa tattalin arziki da raya zaman al'umma.
Wannan shiri yana kunshe da kafa sababbin kauyuka na gurguzu da kyautata tarin masana'antu da samun bunkasuwa cikin daidaici a shiyya-shiyya da raya zaman jama'a mai tsimin albarkatu da kare muhalli da dai sauransu. Wannan shiri kuma ya bayyana manyan tsare-tsare na kasar da muhimman ayyuka da za ta yi da yadda za ta bunkasa tattalin arziki da zaman jama'a, ta haka shirin ya zama wani abu mai muhimmanci ga gwamnatin kasar wajen kula da harkokinta dangane da tattalin arziki da kasuwanci da zaman jama'a da ba da taimako ga jama'a da dai sauransu.(Danladi)
|