Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-06 10:33:34    
Babban dakin baje koli na labarin kasa na kasar Sin

cri
Jama'a masu karatu, yanzu ga shirinmu na game da al'adu na zamani, a cikin wannan shiri za mu gabatar da abubuwan da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana, bayan da ya kai ziyara a babban dakin baje koli na labarin kasa na kasar Sin, sai ga abubuwan da ya ji ya gani daga wannan babban dakin baje koli.

Jama'a masu karatu, in ka yi zauna a nan birnin Beijing cikin dogon lokaci ne sai ya kamata ka yi ziyara a babbar ganuwa da fadar daular sarkin kasar Sin, ban da haka kuma ya kamata ka kai ziyara a manyan dakunan baje koli iri daban daban, daga cikinsu akwai wani babban dakin baje koli na labarin kasa.

A shekara ta l916, an gina babban dakin baje koli na labarin kasa na kasar Sin a nan birnin Beijing, wato wannan babban dakin baje koli na labarin kasa yana da tsawon shekaru 90 daidai. Wato shi ne babban dakin baje koli na kimiyyar halitta na farko da kasar Sin ta kafa. Amma, bayan da aka yi masa gyare gyare da kyautata shi sau da yawa a tarihi, yanzu ya zama wani babban dakin baje koli na zamani.

Jimlar fadin nune nunen wannan dakin baje koli sun kai muraba'in mita 4500, yawan kayayyakin da aka ajiye a wurin nan sun kai fiye da dubu 200.

Wani jami'I na wannan babban dakin baje koli ya gaya wa wakilin reiyonmu cewa, wannnan babban dakin baje koli yana da halayen musamman guda uku, na farko shi ne an ajiye kayayyakin labarin kasa na tarihi da yawa sosai, na biyu kuma an yi bincike kimiyya kan kayayyakin halitta da kuma yin tarbiyya ga dimbin jama'a na zaman al'umma.Ban da haka kuma,ingancin kayayyakin tarihin da aka ajiye a nan yana da kyau sosai,an ce, wannan babban dakin ajiye kayayyakin tarihi na labarin kasa ya fi girma sosai a duk kasashen Asiya. A da masu sha'awar bincike labarin kasa kawai sun yi sha'awar kallo kayayyakin tarihi na labarin kasa, amma yanzu dimbin mutane farar hula su ma suna sha'awar kallo wadannan kayayyakin tarihi na labarin kasa. Ban da haka kuma, wannan babban dakin baje koli na labarin kasa ya kan buga wata mujjala mai suna "Duniya", wannan ita ce daya dayar mujjalar koyar da ilmin labarin kasa na kasar Sin. Wannan babban dakin baje koli na kayayyakin tarihi na labarin kasa ya kan shirya kos iri iri don koyar wa mutane ilmin labarin kasa da ma'anar aikin nan.

A cikin wannan babban dakin baje koli, an kuma ajiye kayayyakin ma'adinai iri iri da duwatsu masu daraja sosai. Yanzu wannan babban dakin baje koli ya yi cudanya tare da shahararrun manyan dakunan baje koli na labarin kasa na kasashe daban daban na duk duniya. Yanzu wannan babban dakin baje koli ya kafa dangantakar aiki tare da na kasar Amurka da na Japan da na Rasha da na Ingila da na Jamus da na sauran kasashe, kuma bi da bi ne tare da nasara ya shirya taron nune nunen kayayyakin labarin kasa na kungiyar wakilan kasar Sin na babban taron labarin kasa na duniya na karo na 26 da na 27 da na 28 da na 29.Kuma a kowace shekara akwai shahararrun masu ilmin labarin kasa na kasashen waje da sukan kai ziyara a babban dakin baje koli da yin musanye musanye ilmin labarin kasa tare da 'yan kimiyya na kasar Sin.

Wani shugaba na wannan babban dakin baje koli ya bayyana cewa, don murnar ranar cikon shekaru 90 da aka kafa wannan babban dakin baje koli, a Bana za a buga litattafai da hotuna da yawa don bayyana wa jama'a ilmin labarin kasar Sin.

Kana kuma ta rediyon mai hoto ne za a bayyana shirye shiryen yin forfoganda ga sha'anin labarin kasar Sin.(Dije)