
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xin Hua na kasar Sin ya bayar, an ce, a cikin 'yan kwanakin nan, Sinawa a ketare da kungiyoyin Sinawa a ketare sun ci gaba da yin tarurukan tattaunawa ko bayar da sanarwoyi domin yin tofin Allah tsine sosai kan matakan neman 'yancin kan Taiwan da Chen Shuibian, jagoran hukumar Taiwan ya dauka. Sannan kuma, sun bayyana cewa, suna la'anta tare da hana aikace-aikacen neman 'yancin kan Taiwan da ake yi. Bugu da kari kuma, sun bayyana cewa, yanzu nauyi mafi muhimmanci da ke wuyan 'yan uwanmu na gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan da dukkan Sinawa a ketare shi ne kiyaye zaman lafiya da na karko a yankin mashigin tekun Taiwan.
Kawancen kungiyoyin kasar Amurka ta yin adawa da yunkurin neman 'yancin kan Taiwan da sa kaimi kan neman dinkuwar duk kasar Sin da kungiyar musayar kasar Amurka wadda ke sa kaimi kan bunkasawa tattalin arziki da kimiyya da fasaha a birnin Shanghai sun bayar da wata sanarwa tare, inda suka yi tir kan kudurin daina aikin "kwamitin dinkuwar duk kasar" da "tsarin ka'idojin dinkuwar duk kasar" da Chen Shui-bian ya dauka. Ana ganin cewa, wannan kuduri tsokana ce ga halin zaman lafiya da ake ciki a yankin mashigin tekun Taiwan.
Sannan kuma, Sinawan da ke da zama a kasar Masar sun yi taron tattaunawa, inda suka nuna cewa, dalilin da ya sa Chen Shui-bian ya dauki wannan mataki shi ne kawo baraka ga dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. Wannan kuduri yana lalata moriyar jama'ar Taiwan kai tsaye. Chen Shui-bian, mutum ne da ke ta da zaune tsaye ga halin zaman lafiya da ake ciki a yankin tekun Taiwan, kuma shi tarnaki mafi tsanani ne ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da neman dinkuwar gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan.
Bugu da kari kuma, Sinawan da ke da zama a kasashen Norway da Portugal da kasar Afirka ta kudu da Venezuala da Singapore da kasar Mali bi da bi ne suka shirya tarurukan tattaunawa ko suka yi tare da gabatar da bayanai domin yin tofin Allah tsine kan matakan da Chen Shui-bian ya dauka. (Sanusi Chen)
|