Firaministan kasar Sin, Wen Jiabao, ya bayyana a yau ran 5 ga wata a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin za ta mayar da kauyuka muhimman wuraren da za a zuba jari wajen raya manyan ayyuka.
Wen Jiabao ya yi wannan furuci ne a yayin da yake bayani a kan aikin gwamnati a gun taron shekara shekara na majalisar wakilan dukan jama'ar kasar Sin, wato hukumar koli ta kasar Sin, wanda aka bude a ran nan. Ya ce, za a karfafa muhimman ayyukan gona a kauyukan kasar Sin, musamman ma bunkasa kananan ayyukan tsaren ruwa, haka kuma za a kara raya tsarin yaki da ambaliyar ruwa da bala'in fari, a sa'i daya kuma, za a kara raya manyan ayyuka a kauyuka, ciki har da gina hanyoyi da samar da ruwan sha da fitar da gas daga shara da bunkasa giza-gizan lantarki da sadarwa, haka kuma za a kara raya muhallin zaman rayuwar dan Adam. Bayan haka kuwa, za a karfafa ayyukan ba da ilmi da kiwon lafiya da al'adu da dai sauran harkokin jama'a a kauyuka. Ban da kara zuba jari ga kauyuka da ayyukan noma, gwamnati za ta kuma sa kaimi ga duk al'umma da su zuba jari a wajen kauyuka da kuma ba da jagoranci a kan batun.(Lubabatu Lei)
|