Ran 5 ga wata da safe, an bude taro na hudu na majalisar wakilan jama'ar kasa ta 10 ta Sin a nan birnin Beijing, inda za a tsai da manufa da manyan matakai da za a dauka don bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin da na zaman jama'arta nan da shekaru 5 masu zuwa.
Mr Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya shugabanci taron, firayim minista Wen Jiabao kuma ya gabatar da rahoto kan ayyukan gwamnati ga wakilan majalisar sama da 2,900. A cikin rahotonsa, Mr. Wen Jiabao ya yi nazarin ayyuka da aka yi a cikin shekarar da ta wuce, ya bayyana shirye-shiryen ayyuka da za a yi, kuma ya yi bayani a kan tsarin ka'idojin shirin bunkasa tattalin arzikin kasa da zaman jama'a a cikin shekaru 5 masu zuwa. Shugabannin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da na gwamnatin kasar kamar Hu Jintao da Jia Qinglin da Zeng Qinghong da Wu Guanzheng da Li Changchun da Luo Gan da sauransu sun halarci bikin bude taron.
A cikin rahotonsa, Mr Wen Jiabao ya bayyana cewa, an kiyasta cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin zai karu da wajen kashi 8 cikin dari a shekarar nan, haka zalika bisa manufar da aka tsaida, nan da shekaru 5 masu zuwa, matsakaicin saurin bunkasuwar nan zai kai kashi 7.5 cikin dari a ko wace shekara. Bugu da kari kuma ya yi bayani mai muhimmanci a kan aikin raya sabon kauyuka na gurguzu da na daidaita batutuwa da suka shafi babbar moriyar jama'a.
Dangane da batun Taiwan, Mr Wen Jiabao ya jaddada cewa, yalwata huldar da ke tsakanin bagorori biyu na zirin teku na Taiwan don tabbatar da zaman lafiya da zama mai karko da samun moriyar juna da nasara tare burin jama'a ne. Tabbas ne, duk wanda ke tauye irin wannan babbar manufar ba zai karasa lafiya ba. Kammala aikin dinkuwar kasar Sin gu daya buri daya ne ga duk Sinawa, kuma ba wanda zai iya hana shi ba.
Da Mr Wen Jiabao ya tabo magana a kan harkokin diplomasiya, sai ya tisa magana cewa, kullum gwamnatin kasar Sin tana bin manufar zaman lafiya game da harkokin diplomasiya cikin mulkin kai kuma ba tare da tsangwama ba. (Halilu)
|