A ran 5 ga wannan wata da safe a nan birnin Beijing, hukumar mulkin koli ta kasar Sin wato Majalisar Wakilan Jama'ar Kasar Sin ta yi bikin bude babban taronta na shekara shekara, a madadin gwamnatin tsakiya, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayar da rahoto dangane da aikin gwamnati ga babban taron. Rahoton ya kasu sassa guda uku, wato waiwayi aikin da aka yi a shekarar da ta shige, babbar dawainiyar da za a yi a shekarar da muke ciki da karin bayani kan babban shiri na 11 na shekaru biyar biyar na raya tattalin arzikin kasa da zamantakewar al'umma, sa'anan kuma ya gabatar da tunanin aiki da babbar manufa ta gwamnatin kasar Sin a cikin shekarar da muke ciki da shekaru biyar masu zuwa. Daga cikin dukan rahoton, muhimmin abu shi ne zaman rayuwar jama'a. Rahoton na da kalmomi dubu 20, kuma ya hada da aikin gwamnati na shekarar da ta shige da shirin shekaru biyar. Amma, muhimmin abu shi ne don bayar da shirin aiki na shekarar da muke ciki, wannan ya bayyana sosai cewa, gwamnati ta mai da hankali sosai ga batun da ya kasance a halin yanzu.
1 2 3
|