A ran 5 ga wata da safe a birnin Beijing, an bude taro na hudu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta goma wato taron NPC a takaice, a gun taron, firayin ministan kasar Wen Jiabao ya bayar da rahoton gwamanti. Kafofin watsa labaru na kasashen waje suna mai da hankali sosai a kan taron, kuma suna bayar da labarai masu nasaba da taron.
Kafofin watsa labaru na Agence France Presse da Reuter da Associated Press da Bloomberg da CNN da dai sauransu sun bayar da labarin budewar taron NPC da na rahoton gwamnati da aka bayar, suna mai da hankali musamman a kan bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin da batun Taiwan da darajar kudin Sin da kafa sababbin kauyuka na gurguzu da dai sauransu. Kafofin watsa labaru na Russian news and information agency da ITAR-TASS na kasar Rasha da na EFERIA na kasar Spain su ma sun bayar da labarin taron NPC cikin lokaci.
Kafofin watsa labaru na Singapore da Japan da Korea ta kudu da India da Pakistan da dai sauran kasashen Asiya suna mai da hankalinsu sosai a kan taron NPC.(Danladi)
|