Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-04 18:33:33    
Kome mugun nufin da aka yi domin balle Taiwan daga kasar Sin zai ci tura

cri

A ran 5 ga wata a nan birnin Beijing, za a bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. A ran 4 ga wata a nan birnin Beijing kuma Jiang Enzhu, kakakin wannan taro ya bayyana cewa, ko kusa babban yankin kasar Sin ba zai yarda da kowane mutum ya kebe Taiwan daga kasar Sin ba, mugun nufin da 'yan jawo baraka na Taiwan ke yi domin balle Taiwan daga kasar Sin ta kowace hanya zai ci tura.

Mr. Jiang ya ce, shugabannin hukumar Taiwan sun yi biris da kiyayyar da mutanen cikin tsibirin Taiwan da na waje ke yi, kuma sun nuna taurin kai kuma sun tsai da kudurin soke "kwamitin dinkuwar kasa daya" da "tsarin ka'idojin dinkuwar kasa daya", wannan ya zama wani taki ne mai hadari da suka yi bisa hanyarsu ta "neman 'yancin Taiwan", kuma ya zama tsokana ce ga ka'idar kasar Sin daya a duniya da ake tsayawa ko'ina a kasashen duniya da zaman lafiya da zama mai dorewa na zirin tekun Taiwan, ba shakka za su samu kiyayya sosai daga wajen 'yanuwanmu da ke gabobin 2 da kakkausar suka daga wajen kasashen duniya. (Umaru)