Ya zuwa yanzu, an riga an share fagen taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da za a fara yi tun daga gobe, wato ran 5 ga wata.
A ran 4 ga wata ne, Jiang Enzhu, kakakin wannan taro ya shelanta wannan labari a nan birnin Beijing. Kuma ya bayyana cewa, a gun taron, wani muhimmin batu shi ne yin tattaunwa da kuma zartas da tsari na shekaru 5 masu zuwa domin bunkasa harkokin tattalin arziki da jin dadin rayuwar jama'ar kasar Sin. Ban da wannan kuma Jiang ya ce, tsarin nan ya bayyana makasudin raya tattalin arziki da jin dadin rayuwar jama'ar kasar Sin na shekaru 5 masu zuwa bisa manyan tsare-tsare, zartas da kuma bin shirin nan zai taka muhimmiyar rawa ga raya tattalin arziki da jin dadin jama'ar kasar Sin daga dukkan fannoni.
Wannan taro da za a rufe shi a ran 14 ga wata za a shafe kwanaki 10 ana yinsa a nan birnin Beijing.(Kande Gao)
|