Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-04 16:53:11    
Yawan rabon da kasafin kudi na tsaron kasar Sin ya dauka bisa na dukkan kasafin kudin kashewa na wannan shekara ya tashi kusan daidai da na 'yan shekarun da suka wuce

cri
A ran 4 ga wata a nan birnin Beijing, Jiang Enzhu, kakakin taron wakilan jama'ar kasar Sin da za a bude a ran 5 ga wata ya fayyace cewa, yawan kudin kasafin kudi domin tsaron kasar Sin da za a gabatar ga wannan taro don zartas da shi ya kai fiye da dala biliyan 35, wato ya kai kashi 7.4 cikin 100 bisa na kasafin kudin kashewa na duk kasar na wannan shekara, idan an kwatanta shi da na 'yan shekarun da suka wuce, sai a ga cewa yawan rabon da ya dauka ya tashi kusan daidai da su.

Mr. Jiang ya kuma fayyace cewa, yawan karuwar kudin tsaron kasar Sin a wannan shekara za a kashe su ne musamman domin kara albashi da kayutata zamna jin dadin hafsoshi da mayakan rundunar soja, sakamakon hauhawar farashin man fetur na kasashen duniya, za a kara yawan kudin kashewa domin sayen man fetur na soja yadda ya kamata, da kara ware kudi da yawa domin horar da kwararrun mutane na soja, da kara yawan kudin kashewa domin sayen kayayyakin soja, ta yadda za a kara karfin tsaron kai da yin fada na rundunar soja. (Umaru)