Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-03 16:59:02    
A karo na farko ne kasar Sin ta bayar da takardar bayani dangane da daidaicin maza da mata da kuma bunkasuwar mata

cri

A ran 1 ga wata, a karo na farko ne kasar Sin ta bayar da takardar bayani dangane da daidaicin maza da mata da kuma bunkasuwar mata. Takardar ta nuna cewa, a shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta sami ci gaba sosai a fannonin lafiyar mata da bunkasuwar aikin ba da ilmi da kuma shiga cikin harkokin tattalin arziki da siyasa da mata ke yi da dai sauransu. Shugabar kungiyar matan kasar Sin, Madam.Gu Xiulian ta bayyana cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta kara tabbatar da babbar manufar nuna daidaici tsakanin maza da mata daga dukkan fannoni na bunkasuwar tattalin arziki da na zaman al'umma, ta yadda za a sa kaimi ga samun daidaicin maza da mata da kuma kyautata harkokin mata.

Wannan takardar da kungiyar matan kasar Sin ta bayar ta yi cikakken bayani a kan bunkasuwar matan kasar Sin a cikin shekaru 10 da suka gabata. Madam.Gu Xiulian ta ce, tun daga shekara ta 1995, kasar Sin ta mayar da nuna daidaicin mata da maza a matsayin wata babbar manufar kasar Sin, don dinga sa kaimi ga bunkasuwar mata da kuma tabbatar da hakkinsu da moriyarsu, sabo da haka, an samar da wani tsari mai inganci da kuma muhalli mai kyau wajen ingiza daidaicin maza da mata. Ta ce, 'a shekaru 10 da suka wuce, a zahiri dai, an kyautata halin da kasar Sin ke ciki a fannonin nuna daidaici tsakanin maza da mata da kuma bunkasuwar mata, an kara ilmantar da mata, haka kuma an inganta lafiyar jikinsu da kuma zaman rayuwarsu. Ban da wannan kuma, an kara daidaita matsayin mata a cikin iyali, an kuma tabbatar da hakkinsu na samun aikin yi, matan kasar Sin sun kara sa hannu cikin harkokin kasa da na zaman al'umma.'

A cikin shekaru 10 da suka gabata, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa da sauri har ya kai sama da kashi 9% a ko wace shekara, kuma matan kasar Sin ma sun ci gajiyar wannan nasara. Ta hanyar sa hannu cikin harkokin tattalin arziki, an daga matsayin mata a zaman al'umma. Ana iya ganin irin wadannan sauye sauye a wurare daban daban na kasar Sin.

 

Alal misali, a jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke arewacin kasar Sin, bisa ra'ayin gargajiya, 'yan kabilar Mongoliya suna ganin cewa, ba abu mai kyau ba ne ga mata da su fita waje su yi ciniki. Amma yanzu ra'ayin nan ya sauya, mata masu dimin yawa sun fita daga gida suna ciniki.

Alatanqimuge, wata makiyayiya ce 'yar kabilar Mongoliya, ita ma tana daya daga cikinsu. Ta yi amfani da dan rancen kudi da gwamnati ta bayar musamman ga mata, ta sayi 'ya'yan tumaki fiye da 10, kuma ta yi cuku ta sayar da su a gari. Ta ce, babban sauyi ta kasance ne a wajen ra'ayi. Da ma mu mata makiyaya ba abin da muke yi sai dai mu bi mijinmu da kuma yara, amma ga shi yanzu, ni ma na iya ciyar da iyalina, sabo da haka, matsayina a iyali ma ba kamar yadda yake a da ba.

Yau a nan kasar Sin, matan da suke ciniki kamar yadda Alatanqimuge ke yi sun zama ruwan dare, kuma ba ma kawai a wajen tattalin arziki ba, a fannonin ba da ilmi da kimiyya da fasaha da siyasa da wasanni da al'adu da kiwon lafiya ne duka suke kokartawa.

Amma duk da haka, akwai wasu matsaloli a wajen bunkasuwar matan kasar Sin a halin yanzu. Lokacin da ta tabo magana a kan batun, Madam.Gu Xiulian ta ce, a sakamakon bunkasuwar tattalin arziki da na zaman al'umma, har zuwa yanzu dai, ya kasance da rashin daidaici tsakanin maza da mata da kuma tsakanin rukunonin mata daban daban, haka kuma akwai al'amura na nuna bambanci ga mata da danne moriyarsu. Bayan haka kuwa, kamata ya yi a karfafa ayyukan mata a harkokin siyasa da kuma wajen yanke shawara.

Madam.Gu ta nuna cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta kara tabbatar da daidaicin maza da mata, don ingiza bunkasuwar harkokin mata.(Lubabatu Lei)