Bisa labarin da wakilanmu suka aiko mana, an ce, ya zuwa yanzu, an riga an share fagen taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa da za a fara yi tun daga gobe, wato ran 3 ga wata.
A ran 2 ga wata ne, Wu Jianmin, kakakin wannan taro ya shelanta wannan labari a nan birnin Beijing. Ya bayyana cewa, a gun taron, membobi fiye da dubu 2 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa za su kara ba da ra'ayoyinsu kan muhimman batuttukan da ke shafar tsari na shekaru 5 masu zuwa domin bunkasa harkokin tattalin arziki da jin dadin rayuwar jama'a. Bugu da kari kuma, za su halarci taron shekara-shekara na majalisar dokokin jama'ar kasar Sin bisa matsayin 'yan kallo, inda za su saurari tare da tattauna rahoton aiki da firayin minista Wen Jiabao zai gabatar a madadin gwamnatin tsakiya.
Wannan taro da za a rufe shi a ran 13 ga wata za a shafe kwanaki 10 ana yinsa a nan birnin Beijin. (Sanusi Chen)
|