Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-02 19:17:13    
Halin da ake ciki a kasar Sin wajen tsabtace gurbatacen ruwa

cri

Kwanan baya tashar tsakiya ta sa ido kan muhallin lardin Shanxi na kasar Sin ta yi kashedi cewa, daga cikin koguna 99 na duk lardin yawancinsu gurbatacen ruwa ne. Daga cikin sassan kogi 99 da da aka yi musu bincike, har da 58 wadanda aka sami kazancewar ruwa mai tsanani, kuma sai sassan kogi 9 kawai da suka kai ma'aunin ingancin ruwa na mataki na farko da na 2 na kasar, wato yawan ingancin ruwan kogin da ya kai ma'aunin kasa ya kai kusan kashi 10 bisa 100 kawai. Ba lardin Shanxi kawai ba, yawan hasarar da aka samu a shekarar 2005 a kasar Sin sabo da gurbatacen ruwa ya karu sosai, wannan ya jawo hankulan duk kasar Sin har da duk duniya baki daya.

Mr. Feng Guangzhi, shugaban hadaddiyar kungiyar shiyyoyin samun moriya daga ayyukan tsare ruwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, "ruwa mafarin rayuwa ne, kuma muhimmin abu ne na muhallin halittu masu rai. Ingancin ruwa muhimmin sharadin zaman rayuwa ne da ya kamata kowa ya more shi, amma ba abun yin bushasha ba ne."

Mr. Ma Zhong, mataimakin shugaban harkokin yau da kullum na kolejin kiyaye muhalli na jami'ar jama'ar Sin ya bayyana cewa, matsalar kazancewar ruwa ba domin dalilin halitta ba, amma sakamako ne da aka samu sabo da dalilin dan Adam da na zaman al'umma da bunkasuwar tattalin arziki.

A gun taron tabbatar da "shirin yin rigakafi da kawar da kazancewar ruwan da ke karkashin kasar Sin" da "shirin kiyaye muhallin mafarin ruwan sha na duk kasar Sin" da aka yi a ran 27 ga watan Disamba na shekarar da ta wuce, kwararru mahalartan taron sun bayyana cewa, cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, tattalin arzikin zaman al'umma na kasar Sin ya samu bunkasuwa da sauri, wannan ba ma kawai ya jawo wadata da ci gaban tattalin arzikin zaman al'umma ba, kuma sabo da har ila yau kasar Sin tana ci gaba da bin wata hanyar da take bi a kullum wato ta mayar da kasar ta zama wata kasa mai masana'antu wajen bunkasa tattalin arziki, yawan albarkatun ruwan da take amfani da su kadan ne, amma gurbtaccen ruwan da aka zubar yana da yawan gaske, wannan ya sa halin da ake ciki a kasar yana da tsanani wajen muhallin halittu da na ruwa.

Mr. Zhang Lijun, mataimakin shugaban babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin ya bayyana cewa, cikin shekaru 25 masu zuwa, kasar Sin za ta gamu da babban matsi wajen muhallin ruwa sabo da za a sami wani sabon zagayen bunkasa tattalin arzikin kasar da sauri, shi ya sa wadannan shekaru 25 za su zama muhimmin lokaci ga kasar Sin wajen hana lalacewar ingancin muhallin ruwa na kasar.

Kwararru sun bayyana cewa, kasar Sin tana nan tana kokarin raya zaman al'umma mai jituwa, muhimmin aikin da za a yi shi ne aiwatar da albarkatun kasa bisa gaskiya da kiyaye muhalli. Amma idan an sadakar da muhalli domin bunkasa tattalin arziki, hakan ba zai iya ci gaba da samun bunkasuwa mai dorewa a kasar Sin ba.

Wani jami'in babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta dauki fasaha ta zamani bisa matsayin ginshikinta, kuma za ta dogara bisa ci gaban kimiyya da fasaha da sa kaimi ga duk zaman al'umma da su shiga aikin kiyaye muhalli, kuma za a bi hanyar kimiyya domin tsara muhimman tsare-tsaren kasa na yin rigakafi da kawar da kazancewar ruwan da ke karkashin kasa da kiyaye muhallin wuraren mafarin ruwa da ake amfani da su, ta yadda za a daidaita matsalar lalacewar ingancin ruwan da ke karkashin kasa da samun ingancin mafarin ruwan sha. (Umaru)