Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-02 18:25:01    
Rogge ya sa ran alheri ga wasannin Olympics da za a shirya a birnin Beijing

cri

A ran 26 ga watan Fabrairu, an rufe wasannin Olympics na lokacin dari a karo na 20 a birnin Torino na kasar Italiya. Da aka gama wasannin Olympics na dari a wannan karo ne, mutanen duniya suka fara mai da hankali a kan wasannin Olympics na lokacin zafi a karo na 29 da za a shirya a birnin Beijing a shekarar 2008. game da haka, wakilinmu na Gidan Rediyon kasar Sin ya yi wata hirar musamman a kan shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Jacque Rogge, Malam Rogge ya bayar da amsoshi dangane da abubuwa da yawa da muke mai da hankali a kai.

Tawagar wakilan 'yan wasa na kasar Sin ta sami nasarori sosai a gun wasannin Olympics na dari na wannan karo. Tawagar kasar Sin ta sami lambar zinariya biyu da ta azurfa hudu da ta tagulla biyar a birnin Torino, ta haka ta zama ta 14 bisa yawan lambar zinariya a duk duniya, game da haka, shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Jacque Rogge ya nuna yabo sosai a kan haka. Ya ce,

'A ganina, kasar Sin ta sami ci gaba cikin sauri. Kafin wasannin Olympics na lokacin dari na wannan karo, kasar Sin ta yi bajimta a gasar da ke kan kankara kawai kamar wasan gudun kankara na gajeren zango. Amma a halin yanzu, kasar Sin ta sami maki mai kyau a kan kankara mai taushi. 'Dan wasa na kasar Sin mai suna Han Xiaopeng ya sami lambar zinariya a gasar freestyle aerials a kan kankara mai taushi?to, wannan ya zama wani mafari mai kyau. Na yi imani cewa, a cikin shekaru da dama masu zuwa, kasar Sin za ta sami nasarori a gun wasannin Olympics na dari kamar yadda take yi a gun wasannin Olympics na lokacin zafi. Dalilin da ya sa na ce haka shi ne domin kasar Sin ta sami ci gaba sosai cikin sauri.'

Muna iya ganin cewa, an sami nasara a ko wane fanni na wasannin Olympics na lokacin dari da aka shirya a birnin Torino. Wannan nasarar ta ya kwamitin wasannin Olympics na duniya ya sa ran alheri sosai ga wasannin Olympics na lokacin zafi a karo na 29 da za a shirya a birnin Beijing a shekarar 2008. Malam Rogge yana ganin cewa, kwamitin wasannin Olympics na Beijing ya koyi abubuwa da yawa daga wasannin Olympics da aka shirya a birnin Torino. A halin yanzu dai, ana gudanar da aikin share fage da kyau game da wasannin Olympics da za shirya a Beijing, amma Beijing yana fuskantar babban kalubale. Malam Rogge ya ce,

'Akwai babban kalubale a gaban birnin Beijing, sabo da ya zama tilas birnin ya sami nasarori a fannoni daban daban, kamar tabbatar da zaman lafiyar 'yan wasa da zirga-zirga da watsa labarai da bayar da hidimar kiwon lafiya da dai sauransu. Wannan zai zama aiki mai wuya domin ya zama tilas birnin Beijing ya sami nasarori a ko wane fanni.'

Malam Rogge ya bayyana cewa, yana sa ran alheri ga wasannin Olympics na lokacin zafi a karo na 29 da za a shirya a birnin Beijing a shekarar 2008, haka kuma ya yi alkawari cewa, kwamitin wasannin Olympics na duniya zai bayar da taimakonsa ga birnin Beijing a ko wane fanni.

Ban da wannan kuma Malam Rogge ya yi yabo sosai a kan shirye-shirye da Gidan Rediyon kasar Sin ta yi dangane da wasannin Olympics, haka kuma yana son nuna godiya ga kasar Sin da ta dukufa wajen bunkasa wasannin Olympics. Ya ce,

'Ina godiya sosai ga abokai Sinawa da su yi kokari a kan bunkasa wasannin Olympics, musamman a kan wasannin Olympics na lokacin zafi a karo na 29 da za a shirya a birnin Beijing a shekarar 2008. A yanzu lokacin yin wasannin Olympics a Beijing bai fi kwanaki dubu daya ba. Ina fata mutanen da abin ya shafa za su ci gaba yin kokari domin samun nasarar wasannin Olympics a Beijing. Ina fata birnin Beijing zai samu sa'a, kuma na gode Beijing!'(Danladi)