Kwanan baya, kwamitin tsakiya na jam'iyyar da ke rike da mulkin kasar Sin wato J.K.S. ya kaddamar da wata muhimmiyar takarda mai suna "ra'ayoyin kwamitin tsakiya na J.K.S. game da kyautata ayyukan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'a". Wannan takarda ta tabbatar da taimako mai ma'anar tarihi da majalisar ta bayar sosai, kuma ta bayyana muhimmanci da wajibcin kara kyautata ayyukan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'a da aka yi bisa sabon halin da ake ciki, da tsara abubuwa da siffofi da kuma hanyoyin da ake bi wajen tafiyar da ayyukan majalisar ta hanyar kimiyya, sabo da haka ta zama takardar ka'ida don jan ragamar ayyukan majalisar. To jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana kan wannan labari.
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin wata hukumar hadin gwiwa da yin shawarwarin siyasa ce tsakanin jam'iyyu da yawa kuma bisa shugabancin J.K.S., kuma wata muhimmiyar hanya ce da ake bi domin yadada dimokuradiyya ta zaman gurguzu da ke cikin zaman rayuwar siyasa na kasar Sin. A gabannin ranar bude taron shekara-shekara na majalisar, an ba da "ra'ayoyin" ta hanyar kaddamar da takardar kwamitin tsakiya na J.K.S., ta zama takardar yin jagoranci ga ayyukan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin. Takardar ta kara tabbatar da hali da matsayi da amfani da kuma ka'idojin ayyuka na majalisar, kuma ta ba da hakikanan ra'ayoyinta kan batutuwan yin shawarwarin siyasa da sa ido kan dimokuradiyya da shiga da kuma ba da shawara kan harkokin siyasa, da kara kyautata ayyukan majalisar, musamman ma ta haifar da sabuwar bukata domin karfafa da kyautata shugabancin da jam'iyyar da ke rike da mulki ke yi wa majalisar.
Mr. Zhang Qia, mamban zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin wanda ya shafe shekaru kusan 20 yana aiki a majalisar, kuma mataimakin direktan kwamitin mutane da albarkatan kasa da muhalli ya gaya wa wakilinmu cewa, "ra'ayoyin" da aka bayar ta hanyar kaddamar da takardar kwamitin tsakiya na J.K.S. ta ba da ra'ayoyi da yin bukata ga kyautata ayyukan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, wannan kuma ya bayyana cewa kwamitin tsakiya na J.K.S. ya mai da muhimmanci sosai kan taimakon da majalisar ta bayar. Ya ce, "Da na dubi wannan takarda, na jiku sosai. Ta zama wata takarda mafi daraja, mafi muhimmanci kuma mafi ma'ana game da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa. Cikin shekaru 20 da suka wuce, an taba kaddamar da takardu da yawa game da majalisar kan yadda za a tafiyar da ayyukan majalisar da kyau, amma wannan takardar da aka bayar ta sha bamban da su, wato a wannan gami kwamitin tsakiya na J.K.S. ya mai da batun kyautata ayyukan majalisar ya zama daya daga cikin abubuwan da take yi domin daga matsayin yin mulki na J.K.S. da raya zaman al'umma mai jituwa, da kuma kara saurin bunkasa tattalin arzkin kasar."
Mr. Zhang ya bayyana cewa, "ra'ayoyin" sun kara yawan abubuwa game da ayyukan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, ya ce, "Takardar ta tanadi hakikanan abubuwa game da muhimman ayyukan da majalisar ke yi wajen yin shawarwarin siyasa da sa ido kan dimokuradiyya, haka ma ga tsarin kungiyarta. Sabo da haka duk ra'ayoyin da aka bayar ta hanyar yin shawarwari tsakanin mutane na sassa daban-daban na majalisar, tabbas ne za su iya samun karbuwa daga wajen sassa daban-daban na jam'iyya da na gwamnatin kasar." (Umaru)
|