Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-02 17:13:06    
Kungiyar sa kaimi kan dinkuwar duk kasar Sin cikin lumana ta yi tofin Allah tsine kan kudurin da Chen Shui-bian ya yi

cri

A ran 2 ga wata a nan birnin Beijing, kungiyar sa kaimi kan dinkuwar duk kasar Sin cikin lumana ta yi taron fadin albarkacin bakinka a nan birnin Beijing, inda aka yi tir kan Chen Shui-bian domin ya tsai da kudurin daina aiki da "kwamitin neman dinkuwar kasa daya" da "ka'idojin neman dinkuwar kasa daya".

Mr. Zhou Tienong, mataimakin shugaban kungiyar ya bayyana cewa, Chen Shui-bian ya yi ko aho da ra'ayoyin neman zaman lafiya da na karko da bunkasuwa na yawancin mutanen Taiwan. Ya yi gasar kacici-kacici da moriyar zaman lafiya ta yankin mashigin tekun Taiwan da ta jama'ar Taiwan domin cimma moriyar radin kansa. Wannan ya kuma kara bayyana cewa yana da miyagun tunaninsa na yin sabon yunkurin kawo baraka ga kasar. Wannan ne kuma ya sake bayyana cewa, a tsibirin Taiwan, Chen Shui-bian mutum ne da ke yin karar-tsaye ga dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan da halin zaman lafiya da ake ciki a yankin Asiya da ke bakin tekun Pacific.

Bugu da kari kuma, Zhou Tienong ya jaddada cewa, neman dinkuwar duk kasar Sin ka'ida ce ta tarihi, kuma makomar da Sinawa ke neman cimmawa. Dukkan Sinawan da suke da zama a duk fadin duniya za su yi tofin allah tsine kan duk abubuwan bata sahihiyar moriyar al'ummar Sin da ake yi. (Sanusi Chen)