Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-02 11:59:53    
Wang Guangya ya gana da babban sakataren M.D.D. da shugaban babban taron M.D.D.

cri
A ran 1 ga wata da yamma, cikin gaggawa ne Wang Guangya, zaunannen wakilin kasar Sin da ke majalisar dinkin duniya ya kai ziyara ga Kofi Annan, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da Jan Eliasson, shugaban babban taro na 60 na M.D.D., inda ya gaya musu cewa gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan batun soke aikin "kwamitin neman dinkuwar kasa daya" da "ka'idojin neman dinkuwar kasa daya" da Chen Shui-bian, jagoran hukumar Taiwan ya yi.

Bayan ya gana da su, Wang Guangya ya gaya wa manema labaru cewa, a gun ganawar, musamman ne ya jaddada cewa, matakin da Chen Shui-bian ya dauka tsokana ce mai tsanani ga ka'idar Sin daya tak da duk duniya ta amince da ita, kuma kalubale ne mai tsanani da Chen Shui-bian yake yi wa halin zaman lafiya da ake ciki yanzu a yankin mashigin tekun Taiwan.

Sannan kuma, Wang Guangya ya ce, lokacin da yake ganawa da Kofi Annan, Mr. Annan ya bayyana cewa, shi ma yana mai da hankali sosai kan hadarin da ka iya faruwa domin jawabin da Chen Shui-bian ya yi. M.D.D. tana tsayawa tsayin daka kan ka'idar Sin daya tak. A wani lokacin da ya dace, a fili ne shi kansa zai bayyana matsayin M.D.D.na yin adawa da matakan da Chen Shui-bian ya dauka. Haka nan kuma, Mr. Eliasson ya jaddada cewa, matsayin da M.D.D. take ciki kan batun Taiwan yana da saukin ganewa. A matsayinsa na shugaban babban taron M.D.D., zai daidaita wannan batu yadda ya kamata.

Daga karshe dai, Wang Guangya ya bayyana cewa, kudurin sosai aikin "kwamitin neman dinkuwar kasa daya" da "ka'idojin neman dinkuwar kasa daya" da Chen Shui-bian ya tsaida tsokana ce mai tsanani ga halin da ake ciki a yankin mashigin tekun Taiwan da halin zaman lafiya da ake ciki a Asiya. Matakan da Chen Shui-bian ya dauka ba za su samu kowane sakamako ba, illa shi da kansa zai kwashi kashinsa a hannu.  (Sanusi Chen)