Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-02 15:34:15    
Sinawan da ke da zama a Amurka sun yi tofin Allah tsine kan Chen Shui-bian

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. A ran 27 ga watan Fabrairu, bayan da Chen Shui-bian, jagoran hukumar Taiwan ya yi shelar daina aikin "kwamitin neman dinkuwar kasa daya" da "ka'idojin neman dinkuwar kasa daya", Sinawan da ke da zama a kasar Amurka sun yi bakin ciki sosai. A ran 28 ga watan Fabrairu, kungiyar Washington DC ta Amurka ta sa kaimi kan yunkurin neman dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin lumana da dalibai da Sinawan da suke karatu da zama a kasar Amurka sun shirya wani taron manema labaru tare, inda suka bayar da wata sanarwar yin suka kan matakin soke "kwamitin neman dinkuwar kasa daya" da Chen Shui-bian ya dauka. Sannan kuma sun yi wa kusoshin hukumar Taiwan kashedin cewa, kada su ta da zaune tsaye, kuma su bata halin neman bunkasuwa cikin lumana da ake ciki a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. Yanzu ga wani bayanin da wakiliyarmu da ke aiki a Washington ta aiko mana.

Mr. Wu Hui-qiu, mataimakin shugaban kungiyar Washington DC ta Amurka da ta sa kaimi kan yunkurin neman dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin lumana ya ce, "Bayan da Chen Shui-bian ya bayar da jawabi a ran 8 ga watan Fabrairu, cewar mutane miliyan 23 na Taiwan ne za su tsai da makomar Taiwan, nan da nan sai kungiyarmu ta bayar da wata sanarwa, inda da kakkausar da harshe ne ta yi tofin Allah tsine kan maganar neman yancin kan Taiwan da Chen Shui-bian ya yi. A sa'i daya kuma, kungiyarmu ta rubuta wasika ga majalisun dokokin kasar Amurka 2, inda aka bayyana bakin ciki da ra'ayoyi game da abubuwan da Chen Shui-bina ya yi domin yunkurin neman yancin kan Taiwan."

Mr. Zhang Wenjian wanda aka haife shi kuma ya yi girma a Taiwan kuma yake aiki a wani kamfanin IT a kasar Amurka ya ce, bisa abubuwan da ya gani da kansa, Chen Shui-bian ya iya yin wasa da kalmomi sosai, kuma yana yaudarar gwamnatin kasar Amurka domin lullube yunkurinsa na neman yancin kan Taiwan. Zhang Wenjian ya ce,

"Jam'iyyar ci gaban Dimokuradiyya ta Taiwan ta taba shirya wani taron tattaunawa kan tsarin mulkin Taiwan. A cikin harshen Turanci dai, ya gaya wa mutanen Amurka cewa ana nazari kan tsarin mulkin Taiwan. Amma a cikin harshen Sinanci kuma, wannan taro ya zama taron tsara tsarin mulkin Taiwan. Takardar da aka rubuta da harshen Turanci da takardar da aka rubuta da harshen Sinanci ba su dace da juna ba. Jam'iyyar ci gaban Dimokuradiyya ta Taiwan da Chen Shui-bian su kan yi irin wannan wasa da kalmomi na baddabami. A ganina, abubuwan da Chen Shui-bian ya yi ba su da amfani a kasashen duniya. Manufar da kasar Amurka take dauka ita ce Sin daya tak. Chen Shui-bian ya iya yin wasu abubuwa a tsibirin Taiwan domin jin dadin magoyon bayansa."

Game da abubuwan da Chen Shui-bian ya yi, madam Lv Mei wadda ta zo daga kungiyar Washington ta sada zumunta a tsakanin abokan aji guda na jami'ar Beijing ta ce, Chen Shui-bian ya yi muggan abubuwa da yawa a cikin wa'adin aikinsa, amma ya yi abubuwan jin dadin jama'ar Taiwan kadan. Madam. Lv ta ce, "Tattalin arzikin Taiwan yana ja da baya, ingancin zamantakewar jama'ar Taiwan ma yana raguwa a kai a kai. Har yanzu mizanin yawan mutanen da suka rasa aikin yi yana da yawa. Chen Shui-bian bai mai da hankali kan ka'idar tarihi ba, ya dauki matakai iri iri domin bambare Sin daga Taiwan. Yana son yanke dangantakar da ke tsakanin al'adun Taiwan da na duk kasar Sin kwata kwata."

A ran 28 ga watan Fabrairu, kungiyar Washington DC ta kasar Amurka da ta sa kaimi kan dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin lumana ta hada da sauran kungiyoyin Sinawa fiye da 100 wadanda suke kasar Amurka sun mika wata wasika tare ga ofishin wakilin tattalin arziki da al'adu na Taiwan da ke Washington, inda suka nemi wannan ofis da ya tsaya a gefen dukkan Sinawan da ke zaune a ketare domin fama da matakan neman yancin kan Taiwan da Chen Shui-bian ke yi. (Sanusi Chen)