Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-02 11:24:25    
An la'anci Chen Shuibian sabo da danyen aikinsa na soke "kwamitin dinkuwar kasar Sin " da "tsarin ka'idojin dinkuwar kasar" a wurare daban daban na kasar Sin

cri
A kwanakin nan da suka wuce a jere, bi da bi kungiyoyi da jaridu da mujalloli na babban yankin kasar Sin da Macao sun nuna kiyewa  tare da yin suka ga Chen Shuibian, shugaban hukumar Taiwan saboda danyen aiki da ya yi na soke "kwamitin dinkuwar kasar Sin gu daya" da "tsarin ka'idojin dinkuwar kasar gu daya".

Shugaban kungiyar hadin kan jama'ar Taiwan ta duk kasar Sin ya bayar da jawabi a ran 1 ga wata cewa, matsannaciyar darikar neman 'yancin kan Taiwan da Chen Shuibian ke gudanarwa ta saba wa burin yawancin jama'ar Taiwan na neman tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun bunkasuwa, kuma ta saba wa babbar moriyar bunkasawar tattalin arzikin Taiwan da zaman karko na siyasa da jituwar zaman jama'a da neman samun zaman lafiya da bunkasuwa a tsakanin bangarori biyu na zirin teku na Taiwan.

Haka zalika shugaban kwamitin tsakiya na kawancen mai cin  gashin kai na dimokuradiyya na Taiwan shi ma ya bayar da jawabi a ran 1 ga wata cewa, irin wannan mataki da Chen Shuibian ya dauka zai kara tsananta halin da ake ciki a yankin Taiwan, kuma zai sa Taiwan ya tsunduma cikin halin mai hadari.

Jarida mai suna "Macao Daily" ta buga ra'ayin edita a ran 1 ga wata inda ta nuna cewa, danyen aikin nan da Chen Shuibian ya yi, ya zama alama ce mai hadari ga tsananta darikar "'yancin kan Taiwan". Hakikanin abu da ya faru ya shaida cewa, Chen Shuibian mutum ne da ya fi haddasa rikici a tsibirin Taiwan da bangarori biyu na zirin teku na Taiwan da kuma shiyyar Asiya da tekun Pacific. (Halilu)