Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-01 19:53:32    
Wasannin Olympics

cri

Wasannin Olympics wasanni ne iri daban daban na duniya da kwamitin wasannin Olympics na duniya ya shirya, kuma a kan yi wasannin a duk shekaru hudu hudu.

Wasannin Olympics ya sami asalinsa ne a tsohuwar Girika. Da can a tsohuwar Girika, a kan shirya wasanni a tsakanin dauloli daban daban. An shirya wadannan wasanni ne don bauta wa gumaka, shi ya sa wasannin ya dauki halin addini, a sa'i daya kuma, an yi wasannin ne don inganta lafiyar jikin jama'a, sabo da an sha samun yake-yake tsakanin daulolin. Amma idan yaki ya barke a lokacin wasanni, to, tilas ne bangarorin da yakin ya shafa su yi shelar dakatar da yaki, sabo da haka kuma, wasannin Olympics suna alamanta zaman lafiya. A kan yi wasannin da suka fi kasaita a wani wurin da ake kira Olympia wanda ke da nisan kilomita 360 daga birnin Athens, sabo da haka, aka sa wasannin suna "Olympics".

An yi wasannin Olympics na karo na farko a shekara ta 776 kafin haihuwar annabi Isa alaihissalam. Ya zuwa shekara ta 393, gaba daya an shirya wasannin Olympics da yawansu ya kai 293. Bayan da tsohuwar daular Rome ta mamaye Girika, sabo da sarkin daular Rome yana bin addinin Krista, sabo da haka, sai ya hana dukan ayyuka na sauran addinai, kuma ya soke wasannin Olympics.

Ya zuwa shekara ta 1888, Pierre De Coubertin, dan kasar Faransa ya ba da shawarar maido da wasannin Olympics, kuma ba ma kawai 'yan kasar Girika ne ke iya shiga wasannin ba, mutane na ko wace kasa na iya shiga wasan duk da kabilunsu da launin fatansu. A shekara ta 1894, an tsai da kudurin kafa kwamitin wasannin Olympics na duniya a gun taron wasannin motsa jiki na duniya da aka yi Paris, daga baya an yi wasannin Olympics na karo na farko a zamanin yanzu daga ran 6 zuwa ran 15 ga watan Afril na shekara ta 1896.

A ran 13 ga watan Yuli na shekara ta 2001, tsohon shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Juan Antonio Samaranch ya shelanta a birnin Moscow cewa, za a shirya wasannin Olympics na shekara ta 2008 a birnin Beijing na kasar Sin. Don shirya wasannin Olympics na shekara ta 2008, birnin Beijing ya gabatar da ra'ayoyi dangane da yaya za shirya wasannin Olympics na Beijing, wato zai kasance wasannin da ke cike da al'adu nagari muhalli mai kyau da kuma fasahohin zamani, kuma a halin yanzu tana kokarin gina dakunan wasa.

A ran 5 ga watan Yuni na shekara ta 2005, an bude shirin masu aikin sa kai na wasannin Olympics na Beijing, an kuma kintata cewa, za a samu masu aikin sa kai kimanin dubu 70, yayin da za a samu masu aikin sa kai dubu 30 a wasannin Olympics na nakasassu.

A ran 26 ga watan nan kuma, an bayyana taken wasannin Olympics na Beijing, wato 'duniya daya, mafarki daya'.

Daga baya a ran 18 ga watan Oktoba, an fara gina gidajen wasannin Judo da Karate na wasannin Olympics na Beijing. To, ya zuwa nan, an riga an fara gina dukan sabbin gidajen wasanni 14 na Olympics.

Daga ran 8 zuwa 11 ga watan Nuwamba na shekara ta 2005, an kira cikakken taron kwamitin daidaita wasannin Olympics na 29 na kungiyar wasannin Olympics na duniya a nan birnin Beijing, inda aka amince da ayyuka masu inganci da kwamitin kula da wasannin Olympics na Beijing ya yi, kuma ake ganin cewa, an cimma burin da aka tsayar a cikakkun tarurruka na da.

A ran 11 ga watan Nuwamba, wato sauran kwanaki 1,000 daidai ke nan da za a bude wasannin Olympics na Beijing, an fitar da alamun fatan alheri na wasannin Olympics na Beijing, wato 'ya'ya biyar masu kawo alheri.

A ran 18 ga watan kuma, kwamitin kula da wasannin Olympics na Beijing ya daddale takardar bayani tare da hukumar muhalli ta MDD. Kafin wannan, kwamitin nan na kula da wasannin Olympics na Beijing ya taba samun lambar yabo kan taimakon da ya bayar wajen kare lemar sararin samaniya. Kwamtin kula da wasannin Olympics na Beijing yana kokarin watsa ra'ayin nan na wasannin Olympics da ke da muhalli mai kyau a yayin da yake shirya wasannin.

To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na amsoshin wasikunku na wannan mako. Muna fatan kun ji dadinsa, kada kuma ku manta mu kan gabatar muku wannan shiri a kowace ranar Lahadi bayan labaru. Da haka, a madadin kowa da kowa, ni Lubabatu ke cewa ku zama lafiya daga nan Beijing.(Lubabatu Lei)