Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-01 17:59:28    
Rushewar "Kwamitin samun dinkuwar kasa daya" da Chen Shuibian ya yi ya samu la'anta da kiyayya daga jama'ar kasar Sin

cri

A ran 27 ga wata da yamma, Chen Shuibian, jagoran hukumar Taiwan ya yi biris da kiyayyar da jama'ar da ke gabobi 2 na zirin teku na Taiwan ke nuna masa, har ya sanar da cewa, an daina ayyukan "kwamitin samun dinkuwar kasa daya" da "tsarin ka'idojin dinkuwar kasa daya". Wannan danyen aikin da ya yi ya jawo la'anta da kiyayya daga ko'ina na gabobi 2. Ra'ayoyin jama'a sun bayyana cewa, Chen Shuibian ya karya alkawarin da ya dauka, kuma ya sa kaimi ga danyun aikin da 'yan kawo baraka na Taiwan ke yi, wannan ya tauye dangantakar da ke tsakanin gabobin 2 sosai, kuma ba shi da amfani ga zaman lafiya da zama mai dorewa da bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobin 2. To, jama'a masu sauraro yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana game da wannna labari.

Bayan da Chen Shuibian ya yi shelar rushe "kwamitin samun dinkuwar kasa daya" da "tsarin ka'idojin dinkuwar kasa daya", a ran 28 ga wata ofishin ayyukan Taiwan na kwamitin tsakiya na J.K.S. da ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa sun sami iznin bayar da sanarwar cewa, danyen aikin da Chen Shuibian ya yi ya sa kaimi ga aikace-aikacen kawo baraka na Taiwan, kuma ya tada hargitsi tsakanin mutanen Taiwan kuma tsakanin gabobin 2 na zirin tekun Taiwan.

Yayin da Mr. Liu Hong, manazarci na ofishin binciken harkokin Taiwan na cibiyar binciken kimiyar zaman al'ummar kasar Sin yake amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi masa ya bayyana cewa, wannan danyen aikin da Chen Shuibian ya yi ya zama wani muhimmin matakin da ya dauka domin neman "samun 'yancin Taiwan bisa doka". Ko da yake ya yi bayani har sau da yawa cewa, ba zai canja halin da ake ciki yanzu a zirin teku na Taiwan daga gefensa kurum ba, amma a hakika kuwa yakan karya alkawarin da ya dauka, da yin aikace-aikacen jawo baraka domin cimma nufinsa na neman 'yancin Taiwan, da yin mugun nufin tada tsokana ga zaman lafiya na zirin teku na Taiwan, kuma ya haddasa matsanancin hali ga dangantakar da ke tsakanin gabobin 2. Mr. Liu ya ce, "Danyen aiki da ya yi ba zai jawo kome ba illa zai jawo rikice-rikice ga Taiwan, ta yadda za a haddasa sabon hargitsi ga dangantakar da ke tsakanin gabobin 2, wannan ya zama wata masifa ce ga zaman al'ummar Taiwan, haka ma ga jama'ar Taiwan. Chen Shuibian wani sanadin sharri ne na haifar da tashin hankali ga zama mai dorewa na Taiwan da na dangantakar da ke tsakanin gabobin 2, kuma shi ne mai tada fitina ga tsibirin Taiwan da dangantakar da ke tsakanin gabobin 2, haka ma ga bangaren Asiya da tekun Pasific.

Mr. Liu Hong, masanin matsalolin Taiwan ya bayyana cewa, wannan danyen aikin da Chen Shuibian ya yi makasudinsa shi ne domin kiyaye matsayinsa daga cikin rukunin 'yan kawo baraka na Taiwan. Amma danyen aikinsa ya jawo matukar hasala daga wajen zaman al'ummar Taiwan. Bisa sabon binciken ra'ayoyin jama'a da kafofishin watsa labaru na Taiwan suka yi a ran 27 ga wata da dare an ce, mutane wadanda yawansu ya kai kashi 20 bisa 100 ne kawai suka nuna goyon baya ga wannan danyen aiki na Chen Shuibian, amma yawancin mutane suna yin adawa da danyen aikinsa. Wani mutumin Taiwan mai suna Huang Xing ya bayyana cewa, "Chen Shuibian wani dan neman 'yancin Taiwan ne kuma mai taurin kai, yana yin mulkinsa cikin shekaru 2 da suka wuce ta hanyar dogara bisa wannan ra'ayinsa kuma ya samu goyon baya daga wasu mutane masu kawo baraka na Taiwan. Ya nuna ha'inci kwarai, kuma yanzu ainihin halinsa na nuna taurin kai wajen samun 'yancin Taiwan ya tonu sosai". (Umaru)