Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-01 16:00:24    
Afirka tana fuskantar hali mai tsanani a wajen shawo kan cutar murar tsuntsaye

cri

Kungiyar kiwon lafiyar dabbobi ta duniya da kungiyar kula da abinci da noma ta majalisar dinkin duniya sun tabbatar a ran 27 ga wata da cewa, an riga an gano mummunar cutar nan ta murar tsuntsaye mai nau'in H5N1 a kasar Nijer. Nijer ta zama kasa ta uku ke nan da aka gano cutar murar tsuntsaye a nahiyar Afirka bayan kasashen Nijeriya da kuma Masar. Masanan da abin ya shafa sun nuna cewa, bisa yaduwar cutar murar tsuntsaye a kasashen Afirka, za a kara fuskantar hali mai tsanani a shiyyar nan a wajen yaki da cutar murar tsuntsaye.

 

Madam. Ilaria Capua, wata jami'ar kungiyar kula da abinci da manoma ta bayyana a gun wani taron duniya dangane da cutar murar tsuntsaye da aka shirya a ran nan a kasar Faransa cewa, binciken da aka yi a dakin gwaje-gwaje na kungiyar da ke kasar Italiya ya nuna cewa, matattun tsuntsayen da aka yi bincike a kansu mummunar cutar nan ta murar tsuntsaye mai nau'in H5N1 ce ta kashe su. An ce, a halin yanzu dai, an tabbatar da bullar cutar murar tsuntsaye a wurare biyu na kasar Nijer, ciki har da birnin Magarya wanda ke dab da kasar Nijeriya. Kungiyar kiwon lafiyar dabbobi ta duniya ta riga ta sanar da sakamakon ga gwamnatin Nijer, kuma ta bayyana cewa, tana son bayar da taimako ga gwamnatin Nijer a wajen yaki da cutar.

Kakakin gwamnatin Nijer Mohamed Ben Omar ya bayyana a ran nan cewa, kungiyoyin da abin ya shafa sun riga sun sanar da gwamnatin Nijer a kan al'amarin, kuma gwamnatin Nijer za ta dauki matakai nan da nan don yaki da masassarar tsuntsaye. Ary Ibrahim, ministan kiwon lafiya na kasar shi ma ya bayyana cewa, gwamnatin Nijer za ta sa kaimi ga makarantu da kungiyoyin addini da su fadakar da jama'a a kan cutar, kuma za su biya manoma diyya don hasarar da suka sha a wajen yaki da cutar murar tsuntsaye.

A ran 8 ga watan nan da muke ciki, an gano cutar murar tsuntsaye mai nau'in H5N1 a kasar Nijeriya, sabo da haka kuma, Nijeriya ta zama kasa ta farko da ta ba da rahoton bullar cutar murar tsuntsaye a nahiyar Afirka. Ya zuwa yanzu dai, an riga an ba da rahoton bullar cutar murar tsuntsaye a yankuna 8 na kasar, ciki har da Abuja, babban birnin kasar. A kasar Masar ma, an gano cutar a yankuna 14.

Bullar masassarar tsuntsaye ta jawo hankulan gwamnatocin kasashen da abin ya shafa da kungiyoyin duniya sosai. Gwamnatin Nijeriya ta kafa cibiyar yaki da cutar murar tsuntsaye nan da nan, don ta kula da ayyukan yaki da cutar. Ban da matakan da aka dauka na kashe dukan tsuntsaye a gonakin da ke wuraren da aka gano cutar murar tsuntsaye da kebe wuraren da kuma hana cinikin tsuntsayen gida a wuraren, gwamnatin Nijeriya ta kuma ware makudan kudade don biyan manoma diyya kan hasarar da suka sha a wajen yaki da cutar murar tsuntsaye. Gwamnatin Masar ma ta dauki matakai masu kyau wajen yaki da cutar.

Ko da yake kasashen da abin ya shafa sun riga sun dauki matakai kamar yadda ya kamata, amma masana sun nuna cewa, dangane da ci gaban yaduwar cutar a nahiyar Afirka, ba za a cimma shawo kan annobar a wurin ba, sai dai bayan wasu lokuta.

Sabo da hali maras kyau da yawancin kasashen Afirka ke kasancewa a wajen kiwon lafiya, ko da yake a halin yanzu dai an bayar da rahoton bullar cutar murar tsuntsaye a wasu yankuna na kasashe uku ne kawai, amma duk da haka, masanan da abin ya shafa suna damuwa da cewa, za a kara samun tasiri daga cutar a kasashen nan uku. Masana sun kuma yi gargadin cewa, mai yiwuwa ne ba kasashe uku na Afirka ne kawai cutar ta bulla ba a hakika, a sa'i daya kuma, mai yiwuwa ne akwai mazaunan wurin da suka riga suka kamu da cutar.

Ban da wannan kuma, manoman Afirka da yawa ba su da isashen ilmi game da magance ciwon tsuntsaye, wanda bai amfana wa ayyukan yaki da cutar murar tsuntsaye a wurin ba. A sa'i daya kuma, don tsoron hasarar kudi da kashe tsuntsaye da yawa zai kawo, manoma da yawa suna ci gaba da cinikin tsuntsaye a asirce duk da dokokin gwamnati na hana cinikin, wanda kuma ya haddasa kara yaduwar annobar.

A sa'i daya kuma, masana sun yi gargadin cewa, bisa nazarin da aka yi, cutar murar tsuntsaye tana sauye-sauye daidai kamar yadda take saurin yaduwa. Idan an samu babbar yaduwar cutar a nahiyar Afirka, to, mai yiwuwa ne cutar za ta kara samun saukin kama dan Adam.(Lubabatu Lei)