Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-01 10:26:01    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(23/02-01/03)

cri
An rufe wasannin Olympic na lokacin hunturu na karo na 20 a birnin Turin na kasar Italiya a ran 26 ga wata. 'Yan wasa fiye da 2500 daga kasashe da yankuna fiye da 80 sun shiga wannan kasaitaccen wasannin da aka yi kwanaki 17 ana yinsa, sun nemi samun lambobin zinare 84. Kungiyar wakilan 'yan wasan kasar Sin ta sami lambobin zinare 2 da azurfa 4 da tagulla 5, ta zama ta 14 a cikin jerin kasashen duniya wajen samun lambar zinare a wannan gami. Wannan karo ne da kasar Sin ta fi samun lambobi tun bayan da ta shiga wasannin Olympic na lokacin hunturu a shekara ta 1980 a karo na farko. Kungiyar wakilan 'yan wasan kasar Jamus ta zama ta farko a wannan gami, saboda samun lambobin zinare 11.

Shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya Mr. Jacques Rogge ya bayyana a birnin Turin a ran 26 ga wata cewa, yana sa ran alheri kan wasannin Olympic na Beijing sosai. Ya kara da cewa, a lokacin da ake yin wasannin Olympic na lokacin hunturu a Turin, jami'an kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing sun yi kallo da koyi kan yadda Turin take shirya wasannin Olympic na lokacin hunturu, sun yi imanin cewa, tabbas ne za su koyi fasahohi masu daraja, wadanda za su taimakawa Beijing wajen shirya wasannin Olympic na shekara ta 2008 lami lafiya.

Akwai wani labari daban game da kwamitin wasannin Olympic na duniya a birnin Turin, an ce, a ran 23 ga wata, wannan kwamiti ya sanar da cewa, kamfanin Johnson&Johnson na kasar Amurka ya zama aboki na 12 da ya yi hadin gwiwa da shi. Kamfanin Johnson&Johnson da kwamitin wasannin Olympic na duniya za su fara yin hadin gwiwa bayan da aka rufe wasannin Olympic na lokacin hunturu na Turin, kafin wannan kuma, kamfanin Johnson&Johnson ya riga ya zama uban tafiya na wasannin Olympic na lokacin hunturu na Turin da wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008 a fannin bayar da kayayyakin kiwon lafiya.

A 'yan kwanakin da suka wuce, a birnin Tokyo na kasar Japan, an yi bikin jefa kuri'a cikin rukuni rukuni domin gasar cin kofin Thomas da Uber ta wasan kwallon badminton ta shekarar 2006, kungiyoyin 'yan wasan kasar Sin maza da mata sun taki sa'a a matsayin zakara na 1, kungiyar maza za ta yi takara da kungiyoyin kasashen Jamus da Indiya a cikin rukuninsa, mata kuma za su yi takara da kungiyoyin Taipei na kasar Sin da Amurka. Kungiyoyin kasar Sin maza da mata za su fito daga rukunnoninsu a matsayin lambawan, saboda karfinsu. Za a yi wadannan muhimman gasannin wasan kwallon badminton a kasar Japan tun daga ran 28 ga watan Afril zuwa ran 7 ga watan Mayu.

Wani jami'in hadaddiyar kungiyar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta kasar Sin ya bayyana a ran 25 ga wata cewa, za a yi gasar fid da gwani ta wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta matasa ta duniya ta karo na 11 a nan Beijing a tsakiyar kwanaki 10 na watan Agusta na wannan shekara, an kiyasta cewa, a lokacin nan, 'yan wasa fiye da 1800 daga kasashe da yankuna fiye da 160 za su shiga wannan gasa. Wannan gasa ce ta koli da kasar Sin ta shirya a fannin wasannin tsalle-tsalle da guje-guje.

Rukunin E ta fara yin gasar zagaye na farko don tace gwanayen da za su shiga gasar cin kofin Asiya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2007 a ran 22 ga wata, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar Palasdinu da ci 2 ba ko daya.(Tasallah)